Abubuwa Biyar da Suka fi Damun ‘Yan Najeriya

 

Yan Najeriya da dama basu damu da mummunan annobar nan ta korona ba.

A bisa ga wani bincike, mutane sun damu da talauci, rashin tsaro da sauransu.

Cibiyar bincike da tuntuba ta Infotrak ce ta gudanar da bincike don shekarar 2021.

Wani bincike ya nuna cewa yan Najeriya sun fi damuwa da wasu abubuwa biyar fiye da mugunyar annobar korona wacce ta kashe fiye da mutane 1,300 a watanni tara da suka gabata.

Binciken da cibiyar bincike da tuntuba ta Infotrak ce ta bayyana hakan a wani bincike da ta gudanar.

A cewar binciken, kaso bakwai cikin dari ne kacal ke nuna damuwa a kan annobar COVID-19 fiye da sauran lamura a 2021.

A bisa ga binciken, ga abubuwan da yan Najeriya suka fi nuna damuwa a kai a shekarar 2021:

1. Rashin tsaro

2. Rashin aikin yi

3. Talauci

4. Rashawa

5. Tsadar rayuwa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here