Abubuwa Game da Ambaliyar Ruwa
Ambaliyar ruwa na shafar birane a fadin duniya, kuma ta zama ruwan dare saboda sauyin yanayi.
Wasu yankuna na birnin Landan da kudancin Ingila sun kasance cikin ruwa tsundum saboda mamakon ruwan sama da aka tafka a watan Yuli.
Mece ce ambaliyar ruwa?
Galibin ambaliyar ruwan na aukuwa ne a lokacin saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya – lokacin da adadin ruwan da zai iya wucewa ta magudanar ruwa ya wuce kima.
Yakan faru ne cikin sauri ba tare da nuna wata alama ba.
Hanyoyi kan kasance a toshe – da motoci da akan bari – sannan da gidaje da shagunan da ambaliyar ruwan ta lalata.
Ambaliyar ruwa kan shafi manyan gine-ginen gwamnati da suka hada da hanyoyin bi na ababen hawa da asibitoci.
A birnin Landan, dole sai da wasu asibitoci suka umarci marasa lafiya da kar su je saboda ba su da wutar lantarki.
Me ya sa tke faruwa a birane da garuruwa?
Yankunan birane kan fuskanci irin wannan ambaliyar ruwan koguna da madatsun ruwa saboda suna kan dandaryar ƙasa masu tauri da ba za su iya tsotse ruwa ba – tun daga daben lambunan shakatawa da na gefen hanya, da titinan kwalta, da na wuraren ajiyar motoci da manyan titunan birane.
A duk lokacin da ruwan sama ya sauka ba za su iya tsotsewa zuwa karkashin kasa ba kamar yadda yake faruwa a kauyuka ko wajen garuruwa.
An ga wani misali a lokacin da aka fuskanci mummunar ambaliyar ruwan Elsa a birnin New York cikin watan Yuli, wadda ta mamaye hanyoyin karkashin kasa.
Shugabar hukumar harkokin sufuri ta birnin Sarah Feinberg, ta bayyana cewa “muddin magudanar ruwan da ke kan titina suka gaza, abubuwa za su kara muni”.
”Ruwan ya malale ta cikin kafofin hanyoyin karkashin kasa har ya zuwa matattakala,” ta ce
A wurare da dama – da suka hada da Birtaniya – an gina hanyoyin magudanar ruwa da dagwalo a bisa has ashen tsarin yadda aka saba samun saukar ruwan sama.
Dr Veronica Edmonds-Brown ta Jami’ar Hertfordshire ta ce bunkasar da birnin London ya yi shi ma ya kara haifar da matsalar saboda tsarin magudanar ruwan irin da zamanin da ne ”ba zai iya jure wa karuwar yawan al’umma ba”.
Shin ana ambaliyar ruwan na kara aukuwa akai-akai?
Abubuwa da dama na haddasa ambaliyar ruwa, amma kuma me yiwuwa sauyin yanayi na kara haifar da saukar ruwan sama mai yawa.
Read Also:
Yanayi mai dumama kan rike karin damshi, don haka ambaliyar ruwan kan kara ta’azzara.
Kamar yadda Farfesa Hayley Fowler, ta Shirin Tunkarar Sauyin Yanayi na Birtaniya ta bayyana, ambaliyar ruwa kan kasance wani ab una ”ba kasafai ba” a baya.
Amma ta ce dumamar na nufin ”wannan mamakon ruwan saman a lokaci kankane daga tsawa mai tsanani da ke haddasa ambaliyar ruwa na kara zama ruwan dare”.
Binciken Miss Fowler yan una cewa ambaliyar ruwan – da ya kai na ma’aunin milimita 30 na kan ko wace sa’a na saukar ruwan sama kan ko wace sa’a – research suggests flash floods – measured as 30mm of rain per hour – ” zai kara linkawa sau biyar nan da shekarar 2080′, muddin sauyin yanayin a cigaba da tafiya a yadda yake.
Me ya kamata a yi?
Za a iya kawo sauyi a garuruwa da birane don kariya daga ambaliyar ruwa mafi muni.
Dakta Linda Speight, wata kwararriya a fannin ambaliyar ruwa a Jami’ar Reading ta ce yankunan birane za su amfana da sauyi kamar na dabe mai tsotse ruwa da korayen rufin kwano da zai taimaka wajen tsotse ruwan sama a maimakon haddasa ambaliya”.
Sanin cewa ruwan mai yawa na shirin sauka za saukaka wajen rage barazanar ambaliyar ruwa.
Dakta Speight ya ce “an samu cigaba cikin sauri hasashen kimiyyar yanayi da kuma ambaliyar ruwa, kana yanzu akwai yiwuwar yin hasashe game da ambaliyar ruwan koguna da tekuna da madatsun ruwa nan gaba “.
Ya zan yi in kare gidana?
Za ka iya dubawa idan yankin da kake yana fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, da kuma alamun gargadin ambaliyar ruwan a shafin yanar gizo na ofishin lura da yanayi.
Kaasancewa nesa da kogi ba lallai yana nufin cewa ka tsira daga ambaliyar ruwan ba.
Ofishin Lura da Yanayi ya bayar da shawarwarin yin tsare-tsare game da ambaliyar ruwa, misali kwashe duk wasu abubuwa masu daraja daga dakunan karkashin kasa zuwa wuraren da babu barazana.
Akwai yiwuwar daukar matakan kariya.
Idan za ka yi sauye-sauye a gidanka ka zabi yin daben zamani a maimakon darduma, kana ka mayar da makunni da soket din wutar lantarki zuwa can saman bango.
Daga nan kuma me ya kamata in yi?
Ya kamata kuma direbobi su rika yin taka-tsan-tsan na kiyaye wa bi ta cikin ruwan, saboda akasarin asarar rayukan da ake dangantawa da ambaliyar ruwa daga motoci ne.
Kamar yadda kamfanin inshora na AA a Birtaniya ya bayyana , sentimita 30 kacal na ruwa ya isa ya yi awon gaba da mota.