Abubuwa Uku da Suka Sammaci ‘Yan Najeriya a 2020
Shekarar 2020 ta zo ma yan Najeriya yara da manya a cikin wata siga da basu saba gani ba.
Shekarar ta zo a baibai wanda ba za a taba mantawa dashi a tarihin kasar ba.
Yayinda kasar ya zo karshe, Legit.ng ta yi amfani da wannan damar wajen duba wasu abubuwan bazata da suka faru a kasar.
1. Zanga-zangar EndSARS
Ko tantama, babu wanda ya sa ran za a yi gagarumin gangamin da matasan Najeriya za su fito su koka a kan cin zarafin da yan sanda ke yi da kuma nman a rushe rundunar yan sandan da ke yaki da fashi da makami wato SARS.
Zanga zangar ya gudana a manyan birane da dama a fadin Najeriya sannan ya ja hankalin kasashen duniya.
Har ila yau, yan Najeriya a kasashen waje irinsu Amurka, Canada, Ingila, Jamus, Ireland da sauran kasashe sun shirya gangamin.
Har ya kai, maudu’in #EndSARS ya zama na daya a batutuwan da suka yi fice a soshiyal midiya.
Read Also:
2. Harbe-harbe da kashe-kashen masu zanga-zangar lumana a Lekki toll gate
Wannan ya kasance daya daga cikin sakamakon zanga-zangar bazatan amma babu wanda yayi tunanin afkuwar abunda aka bayyana da kisan kiyashi a wannan shekarar da wannan karni.
Amma a daren ranar 20 ga watan Oktoba, jami’an rundunar soji su bude wuta a kan masu zangar-zangar lumana a Lekki toll gate da ke jihar Lagas.
Kimanin masu zanga-zanga 12 aka rahoto cewar an kashe a yayin harbin. Rundunar sojin kasar ta musanta yin harbin.
3. Annobar Covid19 Annoba?
Babu wanda ya tsammaci haka a shekarar 2020 amma sai ya afku kuma har yanzu ana cikin wannan hali.
Wannan annoba ta fara ne a 2019 a kasar China amma babu wanda yayi tsammanin cewa zai shafi fiye da mutum miliyan 78.2, lamarin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum miliyan 1.7 a duniya. Annobar ta haddasa hargitsi a mu’amalla da tattalin arzikin duniya. Babu wanda yayi tunanin faruwar wadannan abubuwa uku a shekarar 2020.