Abubuwa 5 da Zan yi in na Gaji Shugaba Buhari – Tinubu

Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina inda ya gana da Gwamna Aminu Masari a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu.

Dan takarar na shugaban kasa a APC ya yi wa wakilai da masu ruwa da tsaki alkawarin cewa zai tura isassun kayan aiki don magance matsalar ‘yan bindiga idan ya gaji Buhari.

Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce zai mayar da hankali ne wajen ci gaba a fannin ilimi da tattalin arziki.

Katsina – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan Legas, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ya yi tsokaci kan abin da wasu ka iya cewa manufofinsa ne na siyasa a shirin zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar na APC na kasa ya bayyana wasu manufofi guda biyar da zai mayar da hankali a kai idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023.

A yayin da yake magana da wakilan jam’iyyar a ranar Litinin a Katsina, Tinubu ya bayyana cewa yana da duk abin da ya kamata na tafiyar da mulkin kasar nan.

A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samo, ya bayyana cewa ya mallaki dukkan wasu abubuwan da ake bukata don a gan shi a matsayin wanda zai iya zama shugaban kasar Najeriya saboda dimbin ilimi da gogewarsa da kuma irin nasarorin da ya samu a harkokin siyasa.

Abubuwan da Tinubu zai yi idan ya gaji Buhari

A ci gaba da haka, Tinubu ya sha alwashin cimma abubuwa kamar haka idan aka ba shi damar mulkar Najeriya:

1. Ka hada kan ‘yan Najeriya da kara musu fata ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

2. Kirkirar sabbin dabaru da kaddamar da isassun kayan aiki don yakar ‘yan bindiga da sauran laifuka masu alaka idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

3. Mai da hankali kan ci gaban tattalin arziki

4. Mai da hankali kan Ilimi.

5. Bunkasa ababen more rayuwa don farfado da Najeriya daga bacci.

A kalamansa, cewa ya yi:

“Na zo ne domin in hada Najeriya ba don in raba ta ba; Na zo ne in kawo muku fata, wadata, farin ciki, aiki, da kwanciyar hankali. Ko da harsuna ka iya bambanta, ’yan’uwantaka zai tsaya; kai dan uwana ne kuma tare za mu fatattaki talauci.”

“Duk wanda yake so zai iya yin takara, amma ba kowa ba ne zai iya zama shugaban kasa ba.”

A nasa martanin Gwamna Aminu Masari ya amince cewa Najeriya na bukatar shugaba mai gogewa kan harkokin mulki.

Gwamnan na Katsina ya kuma bayyana imani da kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta shawo kan kalubalen da ke tunkarar ta nan ba da dadewa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here