Daga: Mansur Ahmed

Adalcin Malam Aminu Kano bai tsaya ga mutane ba kawai, har ga tsuntsaye da dabbobi, shi yasa duk lokacin da yayi jawabi yana cewa jama’a ku yiwa dabbobi da tsuntsaye adalci domin akwai hakkinsu a wuyan mu. Misali wata rana Malam Aminu Kano ya Shiga cikin birnin Kano domin gabatar da ta’aziyya sai ya hangi wani d’an kwuikwiyo a kwance tsananin yunwa ta sa ko tashi baya iya yi sai yara ne suke ta jagwal-gwala shi, sai Malam ya tsaya ya bayar da kudi yace a sayowa karen nan abinci, bayan ya dawo gida tunanin karen nan ya dame shi sai yace to gobe kuma waye zai bashi abinci? Dan haka yasa aka je aka daukko masa karen nan ya kawo shi gidansa har ya saka masa suna Jaura saboda lokacin ana cikin hunturun sanyi.

“”” A takardar barin aikin Malam Aminu Kano da ya rubuta ranar 4 ga nuwamba 1950: “Na hango wani haske a can nesa tsakanin sama da ƙasa. Don haka zan yi kokari in riske shi, ko da a ce ni kadai ne ko da wani.”.

An haifi marigayi Malam Aminu a shekarar 1920 a birnin Kano a Unguwar Dukawa, ya fito daga zuriyar Fulanin Gyanawa mahaifinsa Malamine kuma alkali, ya halarci makarantar Elementary ta Shahuci daga nan ya wuce kwalejin tarayya ta Katsina, Marigayi malam Aminu kano yayi karatun Al-qur’ani mai tsarki a wajen Shehun Malami, Malam Halilu, Malam Halilu shine limamin sarkin Kano Abdullahi Bayero a shekarar 1929 zuwa 1953. Bayan ya gama kwalejin Kaduna ne, Malam Aminu Kano ya samu aikin koyar wa a makarantar Middle da ke Bauchi, inda a lokacin Sir. Abubakar Tafawa Balewa yake a matsayin Hedimasta, Daga Bauchi middle school sai aka canza wa Malam Aminu Kano wajen aiki zuwa kwalejin horar da malamai ta Maru dake Gundumar Sokoto a matsayin hedimasta a shekarar 1949 inda yayi shekara daya a nan kafin daga nan ya ajiye harkar aiki ya kama harkokin siyasa gadan – gadan.

Wani abokin Mallam Aminu kuma almajirinsa a siyasa, marigayi malam Lawan Dambazau a wani d’an k’aramin littafi da ya rubuta a kan tarihin Mallam Aminu Kano, wanda ya sanya wa suna Dan Arewa na ai’nahi Mallam Aminu Kano.” A littafin Mallam Lawan Dambazau ya bayyana abubuwa biyar Mallam Aminu ya kuduri aniya ta fuskar zaman duniya, amma daga karshe babu wanda ya samu, sai a cikin wanda ba ayi zato ba. Ya rayu har ya rasu a ciki wato shugabanci da siyasa.

Da farko ya so ya zama Lauya, amma saboda sanin halinsa sai maganar ta girgiza (Resdan) na Kano na waccan lokacin, domin kowa ya san halin Mallam Aminu Kano na yak’i da akidun turawa na danniyya da zalunci tun yana dan makaranta a “Middle.” Don haka in ya samu dama ya zama Lauya, to zai fituni turawa a kan bakin mulkin mallaka. Saboda haka sai aka dakile maganar ba taje ko’ina ba na biyu; sai ya ce yana so ya zama likita nan ma aka ce babu isassun yaran da za’a hada su, su je Legas makaranatar koyan aikin Likita da ke Yaba; na uku sai ya ce yana so ya yi aikin dan-sanda, nan ma sai aka ce masa tsawon sa bai kai ba da inciKumana hudu, sai ya ce to yana so ya zama malamin asibiti nan ma aka ce a’a sai dai ya yi aikin koyarwa a makaranta. Shi kuma bai cika son koyarwa ba

Gwagwarmayar Mallam Aminu ya fara ne tun yana dalibi a sakandare, Malam Aminu Kano ya fara sansanar harkokin siyasa ne tun a shekarar 1943 lokacin daya taimaka wa Malam Sa’adu zungur suka kafa wata kungiyar siyasa mai suna kungiyar cigaban Bauchi a jihar Bauchi a shekarar 1946. Malam Aminu kano da Malam Sa’adu Zungur sune suka k’arfafa kafuwar jam’iyyar NORTHERN ELEMENT PROGRESSIVE UNION, wadda mutane 8 suka kafa a ranar 8 ga watan 8 a shekarar 1948. Duk da Cewar babu su a zaman tattaunawar ranar

Malam Aminu Kano ya rungumi harkokin siyasa sosai wanda har hakan tasa ya ajiye aikin sa a ranar 4 ga watan nuwamba a shekara 1950. Shekaru 30 Mallam yana jam’iyyar adawa domin fafutukar samarwa talaka ’yanci, ya kubuta daga kangin danniya, zalunci da ake musu a lokacin mulkin mallaka na turawa da kuma bayan an samu ’yancin kai. Masana tarihi a kan rayuwar Mallam Aminu Kano sun ce Malam ya fara koya wa talaka yin tirjiya idan an zalunce shi, kana a karon farko talaka ya fara koyon cewa, a’a a ba ni hakkina a lokacin talakawa suna noma a gandun Sarki kyauta babu kudi

a lokacin da yake aikin koyarwa turawan mulkin mallaka sun yi ta kokarin rufe bakin Mallam Aminu a kan yadda yake fallasa almubazzaranci da ake da kudin haraji. Saboda da haka sai aka tura Malam Aminu Ingila domin ya yi kwas na shekara guda, bayan ya kammala kwas din ya dawo gida maimakon ya yi shiru sai ya ci gaba da caccakar turawa domin a lokacin an hana mahaifinsa Alkali Yusufa ya zama Alkalin Alkalan Jihar Kano, saboda dalilin d’ansa Aminu yana adawa da tsarin mulkin turawa, Malam Aminu kano ya zama shugaban jam’iyyar NEPU na kasa a shekarar 1953 har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki na farko a Nigeria. Ya ta ba cin zabe inda ya zama Dan majalisar tarayya a shekarar 1959 zuwa 1966 inda ya wakilci Kano ta Gabas a karkashin Jam’iyar NEPU, shine mai tsawatar wa a majalisar had’in gwiwa, kuma ya rike kwamishan lafiya na tarayya kuma Dan majalisar zartarwa na koli a gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon.

A karshe Mallam Aminu ya rubuta wani dan karamin littafi mai kunshe da raddi a kan bakin mulkin Turawa. Littafin da ya sanya wa suna {Kano Under the Hammer of the Native administration} duk da haka aka kara yi masa tayin samun malamin jami’a mai koyar da harshen Hausa a jami’ar Oxford da ke Ingila amma Malam Aminu yak’i karba, Mallam Aminu ya bar aikin koyarwa ya kuma tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan. Domin ita ce hanya kadai da zai bi ya kwato wa talaka ’yancin sa, ba tare da ya fuskanci barazana daga Turawan mulkin mallaka ba.

Malam Aminu Kano dashi akai ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula a zamanin Yakubu Gowon wanda Yakubun ya daga bayar da mulkin wanda a dalilin hakan ya haddasa ham’barar da Gwamnatin Gowon din a shekarar 1975 inda Murtala Muhammed ya gaje shi. Da shi akai gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979. Malam Aminu Kano shine shugaban jam’iyar PRP kuma dan takararta na shugabancin kasa a shekarar 1979. Malam Aminu yayi k’aurin suna wajen kin manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwadayi kuma baya siyasar kudi face akida zalla. Kuma makusantan sa wadanda suka yi tarayya da shi a siyasa suka ce a kullum tunaninsa idan garin Allah ya waye, bai wuce abu daya ba, wato yadda za a kyautata zaman jama’a, kana talakan kasa ya san masu shugabancinsa sun san abin da ke damun sa.

Wasu daga cikin mutane sun yi ta yayatawa tare da tunanin akwai rashin jituwa mai karfi tsakanin Malam Aminu Da Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello, da Tafawa Balewa, wannan zance bashi da tushe domin ko bayan rasuwar su an jiyo muryar Malam Aminu a laccoci daban – daban yana yabo da bayyana Sardauna a matsayin mutum mai Amana, Juriya, Jajircewa kuma ya yiwa Arewa abun da ba za’a manta dashi ba,

Ga kwafin wata Wasika da Aminu Kano ya aikawa Sardauna lokacin yana raye

WASIK’A ZUWA GA FIRIMIYAN AREWA, NAJERIYA SIR, AHMADU BELLO A WATAN AFRILU , 1958

                                                                               39 Sudawa, 
                                                                               Akwatin gidan waya 744,
                                                                               Kano.
                                                                                8 ga Afrilu 1958.

Zuwa ga Alhaji Ahmadu Sardaunan Sakkwato,
Ina mai farin ciki shaida maka cewa na sadu da wasik’ar ka a ranar 1 ga wannan wata. Hakika, shirye – shiryen ka da suke cikin wannan takardar, babu shakka za su taimaki musulman kasar nan. Allah ya saka maka da mafificin alheri.
Kuma zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana maka farin ciki na game da irin karbar da kake yi min, da kuma yadda ka nemi da in tuntube ka a kan duk wani batu da na ji zan iya yi a kan haka. Na tabbata wannan zai amfani abokanta kar mu, wadda muka kulla tun lokacin da ba daya daga cikin mu da ya san zai rike wani mukami a gwamnati. Na yi alkawarin ziyartar ka a duk lokacin da Na zo Kaduna komai kuwa irin yanayin aiyyukana
A cikin wasikarka na ga ka kawo wani batu da ya dade a raina, Wadda shine ‘yancin kai ga arewacin Najeriya da ma kasa baki daya, ka tuna da abin da na fada maka a cikin jirgin ruwa kan hanyar mu ta zuwa Landan na ce koda yaushe zan goyi bayan ka a kan maganar yancin kai, ka kira ni a duk lokacin da ka bukace ni zan taimaka a duk wata hanya da zan iya. Amma Ina fatan za ka yi nazari a kan shawararin da zan bayar sannan ka kula da wa su tsiraru da za su yi kokarin biyan bukatun kansu da sunan yancin Kai.
Ina fatan zaka sanar da ni a cikin lokaci duk lokacin da bukatar hakan za ta taso saboda yanayin tafiye – tafiye na.
Ina yi maka fatan kammala azumin watan Ramadan lafiya musamman a cikin wannan yanayi Na zafi. Allah ya shirya mana wannan kasa kuma ya daukaka ta.

                                          Naka.

                                         AMINU KANO. 

TSAKANIN MALAM AMINU DA SARAKUNA DA TURAWAN MULKIN MALLAKA

Al’ummar yankin Arewa a kasar mu Nijeriya lokacin mulkin mallaka da bayan bada mulkin kai sun kasance a wani yanayi da Sarakunan Gargajiya da masu fada aji suka danne talaka da azabtar dashi tamkar bawa a wasu lokutan ma gara bawa kan irin Kama karyar da ake yiwa talaka. Zamanin ya kasance cikin yanayi na danniya da Kama karya da handama da babakere da nauyuka iri-iri na zalunci da aka dankara wa talakawa. Talakawa a lokacin na biyan kudin haraji da jangali da nomau a gonakin masu mulki a kyauta. Wasu lokutan ma in masu mulkin lokacin suka kai rangadi a yankunan dake karkashin su akan tilasta wa magidanci ya bar gidansa da dukkan abunda ya mallaka harma da iyalansa domin saukar dasu da tawagar su!

Malam Aminu Kano ya bayyana ne a tsakiyar lokacin da ake irin wannan zalunci da danne hakkin talaka. Yayi kira ga al’umma dasu bijire tare da kin amincewa da zalunci da kama karyan da akeyi masu tare da mutumta su kamar yan adam masu yanci da martaba. Kafuwar NEPU ke da wuya talakawa suka shiga jam’iyyar babu kama hannun yaro wanda ya jawo tsoro da fargaba ga turawan mulkin mallaka da Sarakunan gargajiya domin akidun NEPU na kira ne ga kawo karshen yadda suke tafiyar da mulkin su na son rai .

Talakawa a lokacin sun amsa kiran NEPU na samun yanci wanda hukumomi su kuma a lokacin suka dauki tsauraran matakai a kansu inda yayi sanadiyar daure tare da azabtar da magoya bayan NEPU. Wasu yan NEPU suka tafi gudun hijira wasu kuma akama sheka dasu barzahu. NEPU karkashin jagorancin Mallam itace jam’iyyar farko a tarihin kafuwar Nijeriya a kasa daya na yunkurin yanto talaka daga mulkin zaluncin fir’aunanci. Mallam Aminu Kano shi ya jagoranci dubban yan gwagwarmayan kwato yanci da wadanda muka sami labarin su da wadanda ma ba’a taba jin su ba muka sami yancin da muke morewa a yanzu. Wasu yan NEPU ma tsire su akayi har suka mutu kamar sannanen labarin Malam Audu Angale. Shi dai an tsire shine a bainar jama’a bisa zargin da akeyi masa na batanci ga Iyayen masu mulki ba tare da gurfanar dashi a gaban Shara’a ba. Haka ma an daura daruruwan yan NEPU ba tare da yi musu Shari’a ba in ma an kaisu gaban Shari’a ba’a basu damar kare kansu kan tuhumar da akeyi masu. Irin wannan zalunci da fin karfi shi yasa wasu yan NEPU in aka kai su gaban alkali sai suce su yan mishan ne domin kotunan basu da hurumin yiwa wanda ba Musulmi ba Shari’a sai a Kai su kotun Nasara inda za’a sake su domin babu shaidun da zasu tabbatar da zargin da akeyi musu.

NASARORIN DA YA SAMU A RAYUWA

Wanne nasarori ya samu a gwagwarmayar sa? Allah ya kaddara masa haddar al-qur’ani Mai girma wadda duk inda zai gabatar da Jawabi da wahala bai kawo aya ya fassara da take da alaka da taron ba, haka Lallai Mallam ya sami gagarumar nasara a gwagwarmayar sa na kawo karshen zalunci. Gwagwarmayar Malam ta tilasta wa Sarakunan gargajiya su sake salon mulkin su tare da kawo karshen nomau kyauta a gonakin masu mulki a kyauta. Ya kuma kawo karshen haraji da jangali. Sannan tsayuwar dakan da Mallam yayi ya baiwa ya’yan talakawa damar samun ilimi zuwa kowanne mataki sannan da rike mukaman siyasa da gwamnati wanda a da ya takaita ne kawai ga gidajen mulki, Yau a Najeriya tun daga kan shugaban kasa har kan wadda yafi kowa kankantar mukami Yayan talakawa ne

A yau a ko’ina a Arewacin Nijeriya mutane na kokarin sanin tare da kare hakkokin su da kundin tsarin mulkin kasa ya basu. Suna kuma shiga cikin harkokin bunkasar dimokaradiya domin cigaban kasar su. A yau akwai yancin fadin ra’ayi ka da walwala wanda masu mulkin mulukiya suka hana al’ummar su a wancan zamanin .

WASU DAGA CIKIN MANYAN ABOKAN GWAGWARMAYAR SA.

  1. Malam Sa’adu Zungur
  2. Bello Ijumu
  3. Musa Kaula
  4. Baballiya Manaja
  5. Alhaji Adamu Danjaji
  6. Magaji Dambatta
  7. Mudi Sipikin
  8. Malam Abba Mai kwaru
  9. Malam Illah Ringim
  10. Muhammad Danjani Hadejia
  11. Malam Audu Angale
  12. Alhaji Dauda Dangalan
  13. Hajiya Asabe Reza
  14. Hajiya Gambo Sawaba
  15. Malam Lawal Dambazau
  16. Mrs. Bola Ogunbon
    Da sauran su da dama

An saka sunan Malam Aminu Kano a, Filin jirgin saman ƙasa da ƙasa dake kano, Asibitin koyarwa na kano, Aminu Kano Legal, Filin taro na Aminu Kano Triangle A Jigawa, Titin Aminu Kano Way a Kano, Jigawa, Lagos, Bauchi, Kaduna Da Abuja

Ya rasu ya bar mata daya, Aishatu. Wadda Allah ya yiwa rasuwa ranar /22/5/2017 da ’yar sa daya Maryam. Sannan ya bar gida daya da gona. Allah ya jikan Mallam

The post Abubuwan da za a tuna Malam Aminu Kano: Shekaru 36 bayan mutuwarsa appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here