Kungiyar ACF ta yi Allah-Wadai da Luguden Bam Kan Fararen Hula a Kaduna
Kungiyar dattawan Arewa (ACF) ta yi Allah-wadai da harin da aka kai da jiragen yaƙi marasa matuka a yayin wani taron mauludi a unguwar Tudun Biri, jihar Kaduna a ranar 3 ga Disamba, 2023
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar inda ta buƙaci da a gudanar da cikakken bincike na gaskiya kan lamarin.
Ƙungiyar ta kuma bayyana lamarin a matsayin rashin ƙwarewa wajen tattara bayanan sirri.
Rundunar sojin Najeriya dai ta amince da kai harin, inda ta bayyana shi da “rashin hankali”. Rahotanni sun nunar da cewa an samu asarar rayuka, inda mutane kusan 80 galibi yara da mata ne ke fargabar sun mutu tare da jikkata wasu da dama.
Ƙungiyar ta bukaci sojoji da su fito da cikakkun bayanai don magance fargabar jama’a.
Read Also:
“Muna baƙatar a yi cikakken bincike, ta hanyar gaskiya da bude ido kan lamarin, don tabbatar da hakikanin abin da ya faru da wadanda ke da hannu da kuma fayyace adadin rayukan da aka rasa da kuma jikkata; Da dai sauransu. Kuma Duk wanda aka samu da laifin ko ƙwararru ko gazawar aiki dole ne a hukunta su sosai” in ji sanarwar
“Ya zama wajibi gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin kare muradun wadanda abin ya shafa ba jami’an sojin Najeriya da suka aikata wannan aika-aika ba.”
“Dole ne a biya diyya ga iyalan waɗanda suka mutu daidai da darajar diyya ta Musulunci”
“Domin dawo da kwarin gwiwar jama’a, dole ne sojojin Najeriya su nemi afuwar al’ummar ƙasar da lamarin ya shafa. Bugu da kari, a matsayin alamar gaskiya, ya kamata sojojin Najeriya su gaggauta gudanar da ayyukan jinya da sauran ayyukan farfado da al’umma a cikin al’umomin da abin ya shafa.”
“Ya kamata babban hafsan tsaro ya umarci dukkan jami’an soji da su samar da ingantacciyar dabara don gujewa tabarbarewar abubuwan da suka faru a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.”, sanarwar ta ƙara da cewa.