ACF ta Fadi Sabuwar Hanyar da Ake Shigo da Makamai Najeriya
Kungiyar dattijan arewa (ACF) ta kwarmata cewa yanzu an koma amfani da Rakuma wajen shigo da makai.
ACF ta bayyana cewa mambobinta daga jihohn Sokoto da Zamfara ne suka sanar da ita hakan.
A cewar ACF, alhakinta ne ta fasa kwai, ta sanar da gwamnatin tarayya domin daukan matakin da ya dace.
Babbar kungiyar zamantakewa da siyasa, kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), ta kwarmata cewa yanzu da rakuma ake amfani wajen shigo da makamai yankin arewa.
Read Also:
ACF ta bayyana cewa ana amfani da Rakuma wajen safarar manyan bindigu na RPG da bindigun harbo jirgin sama zuwa Nigeria ta kan iyakokin da ke arewa, kamar yadda Punch ta rawaito.
Cif Audu Ogbeh, shugaban ACF, shine ya bayyana hakan a cikin wani jawabi mai dauke da sa hannunsa wanda ya fitar ranar Alhamis.
Cif Ogbeh ya bayyana cewa ana shigo da makaman ne daga makwabciyar kasa, amma bai ambaci sunan kasar ba.
ai dai, ACF ta ce mambobinta daga jihohin Sokoto da Zamfara ne suka sanar da su hakan.
Najeriya ta yi iyaka da kasar Nijar ta bangaren jihohin Sokoto da Zamfara.
Shugaban na ACF ya bayyana cewa alhakin kungiyar ne ta sanar da gwamnatin tarayya wannan bayani domin daukan matakin da ya dace.
Cif Ogbeh, tsohon ministan noma, ya ce ‘yan bindiga na samun kudin siyen makamai daga kudaden biyan fansa da suke tatsa daga hannun jama’a.