Kungiyar ACF ta Magantu Kan Sace Dalibai 73 a Jahar Zamfara

 

Kungiyar Arewa Consultative Forum ta yi Allah wadai da sace dalibai guda 73 da wasu ‘yan bindiga suka yi a jahar Zamfara.

ACF ta bayyana cewa babu wani amfani a wanzuwar gwamnati da ba za ta iya kare al’ummanta ba.

A ranar Laraba, 1 ga watan Satumba ne dai ‘yan bindigar suka kai farmaki wata makaranta da ke karamar hukumar Maradun ta jahar Zamfara sannan suka yi awon gaba da dalibai da dama.

Kaduna – Kungiyoyin Arewa Consultative Forum, da Southern Kaduna Peoples Union sun yi Allah wadai da sace dalibai 76 da wasu ‘yan bindiga suka yi a jahar Zamfara a jiya Laraba, 1 ga watan Satumba.

Sakataren yada labarai na kungiyar ACF, Emmanuel Yawe, ya bayyana bakin cikinsa kan sabon harin da sace daliban.

Kakakin na ACF ya shaida wa jaridar Punch a Kaduna, a ranar Laraba, cewa kungiyar ta arewacin kasar ba ta jin dadin ayyukan ‘yan fashi da ke gudana a yankin.

Duk gwamnatin da ba za ta iya kare ‘yan kasa ba ba ta da amfani – ACF

Yawe ya bayyana cewa duk gwamnatin da ba za ta iya kare ‘yan kasarta ba toh lallai ba ta da wani amfani na wanzuwa.

Ya ce:

“To, wani mataki Matawalle ya dauka? Bai kamata mutane su yi sanarwa ba kawai. Idan yana kira ga jama’a su tashi su kare kansu, ya kamata ya iya yin kari a duk kokarin da jama’a ke yi.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here