Shugaba Buhari ya Bayyana Adadin Gidajen da za su Samu Wutar Lantarki a 2030

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gidaje miliyan biyar za su samu lantarki a wani babban shirin gwamnati na samar da makamashi zuwa 2030.

Shugaban ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa kan makamashi da aka gudanar a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana a cikin wata sanarwa.

A cewar Shugaban, Najeriya ta kaddamar da shirin samar da lantarki ga gidaje miliyan biyar da kuma mutum miliyan 20 ta hanyar da amfani da makamashin hasken rana.

Ya ce wannan mataki ne na farko da cike gibin samun makamashi zuwa 2030.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here