Kyamar Musulmi ta fi Muni Kuma Tana Yaduwa a India – Firaministan Pakistan

 

Firaministan Pakistan Imran Khan ya zargi India a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kyamar addinin Islama.

Wadannan Kalaman sun janyo martani mai zafi daga wakilan India.

Imran Khan ya zargi Firaministan India Narendra Modi da kokarin ‘kawar da musulmin India.” A cikin jawabinsa na bidiyo, ya kara da cewa “kyamar musulmi ta fi muni kuma tana yaduwa a India” kuma ya hada da musulmai kusan miliyan 200 da ke India.

Khan ya zargi hukumomin Amurka da nuna amincewa da “take hakkin dan Adam da India ke yi”, yayin da kuma jawabin Imran Khan ya yi daidai da tarbar Nerandra Modi a Fadar White House.

A lokacin ganawarsa da Biden, Modi ya bayyana damuwa kan rawar da Pakistan ke takawa da Afghanistan.

Imran Khan a cikin jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya ce Taliban ta yi alkawalin za ta kiyaye hakkin dan Adam da kuma karfafa guiwar kasashen duniya su kulla yarjejeniya da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here