Somalia: An Kai Harin Bom Kusa da Fadar Shugaban Kasa a Mogadishu 

 

 

Wata mota makare da bama -bamai ta tashi kusa da fadar shugaban kasa a Mogadishu, babban birnin Somalia.

Kafafen yada labarai na cikin gida sun ce an kai harin ne a dogon jerin motoci a wani shingen bincike na jami’an tsaro.

An samu rahotannin da ke cewa mutane sun mutu kuma wasu sun jikkata.

Kungiyar masu kishin Islama ta Al Shabaab ta ce ita ta kai harin.

Kungiyar ke da iko da manyan yankuna na kudanci da tsakiyar Somalia kuma a kai a kai tana kai hare-hare a yankunan da ke karkashin ikon gwamnati, musamman ma Mogadishu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here