Adadin Mutanen da Hatsarin Jirgin Ruwa ya Kashe a Cikin Shekara 3 a Najeriya

 

Aƙalla mutum 936 ne suka mutu a hatsarin jirgin ruwa daba-daban da suka faru a Najeriya cikin shekara uku.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƙarancin hanyoyin cikin ruwa marasa yayi da kuma ɗaukar fasinjoji da suka wuce iyaka na daga cikin matsalolin dake janyo wannan lamari.

Hakan ya sa a ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan yawan kifewar kwale-kwale a Najeriya da yake neman zama ruwan dare.

Masana dai na ta bayar da shawara cewa ya kamata mahukunta su ɗauki matakin da ya wuce na furtawa da fatar baki kawai a gani a aikace don a shawo kan wannan matsala.

Sun kuma bayar da shawara kan cewa kamata ya yi a maye gurbin kwale-kwalen da ake da su na gargajiya da na zamani, domin ci gaba da sufuri da su.

A Najeriya dai sufuri ta hanyar jirgin ruwa na gudana ne a hannun mazauna ƙauyukan da ruwan yake, abu ne da gwamnati ba ta mayar da hankali a kai ba, wanda hakan ya sabawa ka’idar aikin da aka shimfiɗa a duniya.

Haɗarin da ya faru a makon jiya ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 20, ya janyo wa hukumomin da ke lura da sufurin jiragen ruwa suka na rashin mayar da hankali kan abin da ke gudana arewacin Najeriya da Allah ya albarkanta da tafkuna da kuma ƙoramu.

Sai dai kullum hukumomi na iƙirarin suna iya ƙoƙarinsu domin daƙile wannan matsala.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com