Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Korona Ranar Talata
A ranar Litinin an dan samu sauki, mutane 397 suka kamu da cutar Korona.
Amma ranar Talata bata yi kyau ba yayinda aka koma inda aka fito.
Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasar Amurka da Ingila ba.
Mutane 749 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.
Read Also:
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 85,560 a Najeriya.
Daga cikin sama da mutane 85,000 da suka kamu, an sallami 71,937 yayinda 1267 suka rigamu gidan gaskiya.
Wani sabon nauyin cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.
Ga adadin jiha-jiha:
Lagos-299
Plateau-131
Kaduna-83
FCT-74
Kwara-35
Sokoto-26
Edo-18
Kano-17
Katsina-16
Delta-11
Nasarawa-10
Ondo-9
Bauchi-9
Rivers-5
Akwa Ibom-3
Jigawa-1
Osun-1
Ekiti-1