Rashin Tsaro: Adadin Mutanen da Jahohi Suka Rasa a 2020

An fuskanci matsalar tabarbarewar tsaro a cikin shekarar 2020 da ta gabata.

‘Yan bindiga, ‘yan fashi da makami, masu garkuwa mutane da kuma ‘yan Boko Haram sun hallaka dumbin mutane.

Kididdigar jaridar TheCable ta nuna cewa ‘yan Nigeria 3,326 ne suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci a shekarar 2020.

Wata Kididdigar alkaluma da jaridar TheCable ta wallafa ta nuna cewa ‘yan Nigeria dubu uku da dari uku da ashirin da shidda (3,326) ne suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci.

Alkaluman sun nuna cewa jahohin Borno, Kaduna, Katsina, Zamafara, da Benuwe sune a sahun biyar na farko da aka fi samun asarar rayuka.

Jahohin Gombe, Kebbi, Enugu, Jigawa, da Kano sun kasance jahohi biyar mafi karacin yawan salwantar rayuka sakamakon ayyukan ta’addanci.

Rayukan mutane 665 aka rasa a jihar Borno sakamakon hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda.

Alkaluman sun nuna cewa rayuka 489 sun salwantar a jahar Kaduna, 375 a jahar Katsina, 219 a jihar Zamfara, sai kuma in mutane 156 a Benuwe.

TheCable ta ce alkaluman basu hada da adadin mutanen da ‘yan fashi da Jami’an tsaro suka kashe ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here