Matsalar Tsaro: Gwamnatin Adamawa ta Rufe Makarantun Kwana 30 Dake Jahar
Jahar Adamawa ta rufe wasu makarantun sakandare saboda ta’azzarar lamurran tsaro a kasar.
Gwamnatin jahar ta bayyana haka ne ta bakin kwamishinan ilimi na jahar ta Adamawa a fadar jahar.
Gwamnati ta kuma bayyana cewa, hakan wani yunkuri ne na kare dalibai daga fadawa hadarin ‘yan bindiga.
Adamawa – Gwamnatin jahar Adamawa ta sanar da rufe makarantun sakandire na kwana 30 da ke jahar daga cikin kananan makarantu 34 saboda matsalar rashin tsaro.
Rufewar, a cewar wata sanarwa daga kwamishiniyar ilimi , Mrs. Wilbina Jackson, za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Satumba, 2021 har sai an sake samun wani ci gaba.
Read Also:
Sanarwar da wakilin jaridar Punch ta gani ta ce daukar wannan mataki wani yunkuri ne na tabbatar da tsaron dalibai saboda rashin tsaro da ke addabar kasar.
Matakin na gwamnatin jahar ya zo ne a yayin da ake ci gaba da samun karuwar ‘yan bindiga a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar sace daruruwan yara ‘yan makaranta a jahohi da dama.
Makarantu hudu da rufewar ba za ta shafa ba sune Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnati dake Yola; Kwalejin Janar Murtala Mohammed ta Yola; Makarantar Jada ta Musamman; da Makarantar Mubi ta Musamman.
Wani yankin sanarwar ya kara da cewa:
“Wannan ya zama dole saboda kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu da kuma duba da karancin shekarun dalibai, saboda haka ake bukatar su yi karatu karkashin kulawar iyayensu.
”Za a sanya dukkan daliban makarantun da abin ya shafa a makarantun sakandaren gwamnati mafi kusa da su a cikin wuraren da suke da zama. Masu ruwa da tsaki, PTA, ANCOPS da sauran su za su tabbatar da bin wannan manufar ta gwamnati.”