Jam’iyyar APC ta Karyata Batun Zanga-Zangar Nuna adawa da Buhari a Landan

Jam’iyyar APC ta karyata hotunan da ke yawo ana ikirarin zanga-zangar nuna adawa da Buhari a Landan.

Jam’iyyar ta bayyana asalin inda aka dauko hotunan, tare da bayyana ranan da aka daurasu.

Hakazalika ta shawarci wanda ya watsa hotunan cewa ya sani wannan zunzurutun karya ne Jam’iyyar APC reshen kasar Ingila, ta karyata wani labarin karya na kafofin sada zumunta cewa wasu ‘yan Najeriya sun mamaye gidan da shugaba Buhari yake a Landan don nuna adawa da Shugaban.

Jaridar Punch a jiya ta ruwaito cewa shugaban ya tashi daga Najeriya zuwa Landan inda zai kwashe makonni biyu domin duba lafiyarsa.

Wani a dandalin Twitter, @Tqswaggerboi, ya watsa hotunan wasu masu zanga-zanga tare da ikirarin cewa suna jiran isowar Buhari Fadar Najeriya ne a Landan.

“Daruruwan masu zanga-zanga da asalinsu ‘yan Najeriya ne sun mamaye Fadar Najeriya da ke Landan, suna jiran isowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke zuwa ziyarar duba lafiya na makonni biyu.

#BuhariMustGo,” ya sanya tare da hotunan.

A martanin da ta mayar game da hotunan, APC ta ce, “Don Allah ka sani cewa @Tqswaggerboi rubutunka na karfe 7.54 na safe LABARIN KARYA ne!”

Jam’iyyar ta watsa likau zuwa gidan yanar gizon da aka samo hotunan, wanda ke nuna cewa ba kwanan nan aka dauke su ba, asalinsu daga sigar Burtaniya ta zanga-zangar #EndSARS ta Oktoban bara ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here