Ma’ikatar Jin Kai da Agaji ta Kaddamar da Siyasar Kasa Akan IDP Kunshe da Kafafen Yaɗa Labarai Zuwa shirin Budaddiyar Gida na Ma’aikatar

Ministan kula harkokin jin kai agajin gaggawa da inganta rayuwar al’umma, Sadiya Umar Farouq ta kaddamar da manufar kasa kan ‘yan gudun hijirar a ranar Talata.

Takardar kaddamarwa, wacce Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ita a watan Satumbar 2021 an kaddamar da ita ne a Abuja a shirin taron budaddiyar gida na Ma’aikatar jin kai, mai taken “Haɗin kai don Dorewar ayyukan jin kai da agaji” Tafiyar da akayi.

Ministan ta bayyana cewa, an yi la’akari da sababbin al’amura da kuma abubuwan da suka kunno kai a fannin jin kai a Najeriya kafin bullo da aiwatar da manufar.

“Wannan manufar yazo da nufin samar da tsarin alhakin ƙasa na rigakafi da kare lafiyar ‘yan ƙasa da kuma, a wasu lokutan, ma harda waɗanda ba ‘yan ƙasar ba, daga abubuwan da ke faruwa na son rai dama sauran nau’o’in gudun hijira na cikin gida, da biya musu bukatunsu tare da basu kariya a lokacin hijira, da kuma tabbatar da rayuwarsu, da sauran duk wasu nau’in agaji a yayin ƙaura.

Manufar ita ce ta fitar da ka’idojin da za su jagoranci taimakon jin kai da aiwatar da hanyoyin da za a bi wajen magance rikicin cikin gida a Najeriya, kuma ta yi amfani da tsarin kare hakkin bil’adama da ka’idojin su.”

Ministan ta kuma ba da tabbacin cewa, ana ci gaba da tsare-tsare na gudanar da taron Kampala na kungiyar Tarayyar Afirka.
Ina so in sanar da cewa a hukumance mun fara aiki na kai tsaye na shigar da yarjejeniyar Taron Kungiyoyin Tarayyar Afirka Kampala.

Ana umartar masu ruwa da tsaki da su fito da daftarin lissafi don gabatar da shi ga hukumar ta FEC domin amincewa da kuma mika shi ga Majalisar Dokoki ta ƙasa domin daukar matakin da ya dace.

Don tabbatar da ingantaccen aiki da aiwatar da manufofin kasa game da IDP. An kaddamar da kwamitin ayyuka na ƙasa da ƙasa tare da umartar sauran masu ruwa da tsaki da su fara ba da cikakken bayani kan shirin aiwatarwa tare da bayyanannun ayyuka da nauyin da ya rataya a wuyan dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da dabarun sa ido da tantancewa. wanda zai tabbatar da bin tsarin manufofi da iyakoki, da kuma tantance iyakar cimma manufa.

A tun farko, ministan ta bayyana cewa Kaddamar da budaddiyar taron jin kai an yi shi ne da nufin baje kolin shirye-shirye da ayyukan da ma’aikatar ta yi a cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

“Yau rana ce ta musamman da ma’aikatar ta kebe domin tattaunawa da ‘yan jarida, abokan hulda da masu ruwa da tsaki tare da ba su damar yin tambayoyi, samun karin haske da bayar da shawarwari masu amfani ta hanyar jin ra’ayoyinsu.

Shirin Budaddiyar gidan Taron jin kai zai karfafa zumunci don tattaunawa da musayar ra’ayi don baiwa kwararrun kafofin watsa labarai damar ba da rahoto mai inganci, tare da kuma samar wa masu ruwa da tsaki da abokan hulɗa, bayanan farko don yaɗawa a kafafe daban daban.

Ministan Sadiya Umar Farouq ta gabatar da kasidar bayanai na Ma’aikatar da kuma kasidar bayanai ta (NSIP) wato shirin zuba jari na ƙasa ga jama’a.

ƙasidar littafin bayanai, yana ɗauke da duk bayanai game da Ma’aikatar, Sashenta, Shirye-shirye da Hukumomi.

Hakazalika, an kuma kaddamar da wani babban taro na hoto mai dauke da shirye-shirye, ayyuka da nasarorin da ma’aikatar ta samu, yayin da Ministan ta zagaya da bakin da suka ziyarci rumfunan agaji.

Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da sakon fatan alheri, wanda ya samu wakilcin Hon Muhammad Jega, da babban sakataren ma’aikatar Bashir Nura Alkali wanda ya samu wakilcin daraktan ayyukan jin kai, Alhaji Ali Grema da kuma ko’odinetan Majalisar Dinkin Duniya Matthias Schmale wanda ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa ma’aikatar a yankunan da suka shafi ‘yan gudun hijira.

Sauran jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar, CSOs/NGOs, shugabannin kungiyoyin NSIP, daraktoci a ma’aikatar, abokan hulda, Editoci da masu aika rahotannin jin kai.
NNEKA IKEM ANIBEZE
SA MEDIA
22-03-2022

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here