AFAN: Muna Rokon Shugaba Buhari da Kar a Bude Boda
Ministar Kudi ta ce sun baiwa shugaba Buhari shawara ya bude iyakokin Najeriya.
An rufe iyakokin ne tun watan Agustam 2019 don hana shigo da kayayyaki.
Manoman Najeriya sun nuna mabanbancin ra’ayi kan shirin sake bude iyakokin Manoman Najeriya a ranar Laraba sun yi Alla-wadai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sake bude iyakokin Najeriya na kasa.
Sun bayyana cewa bude iyakokin a yanzu da kayan abinci ke hauhawa abune mai hadarin gaskiya.
Read Also:
Sun ce kasashe makwabta da suka dogara kan Najeriya wajen samun kayan abinci zasu shigo kasar kuma hakan zai sa kayan abinci ya sake hauhawa, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN) Arch. Kabiru Ibrahim, ya bayyanawa DT a hirar wayar tarho cewa bude bodan zai saukaka fitar da kayan abinci daga Najeriya zuwa kasashe masu makwabtaka da mu.
“Kuna ganin yanzu ana noma ana girba amma duk da haka kayan abinci na hauhawa saboda wasu dalilai,… inaga idan aka bude iyakokin, abin da hadari, ” yace.
Manoman sun kara da cewa a tuna har yanzu akwai annobar cutar Korona kuma bari mutanen daga wajen sun shigowa Najeriya na iya kara harzuka kamuwar cutar a nan.