Kungiyar Afenifere ta yi Alla-Wadai da Zaɓen Tinubu

 

Pa Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ya mayar da martani kan ayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Yayin da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da BBC, Adebanjo ya bayyana zaɓen da ya bai wa Tinubu nasara a matsayin mai cike da kura-kurai.

Ya ce sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma hakan na iya haifar rikici a ƙasar.

Adebanjo ya ce gazawar da INEC ta yi na amfani da na’urar BVAS a rumfunan zaɓe kamar yadda ta yi alkawari tun da farko, ya nuna cewa wasu sun tsara yadda zaɓen zai gudana da kuma ɗan takara da suke so ya yi nasara.

Ya ƙara da cewa a iya saninsa, shi dai ba a gudanar da zaɓe a ƙasar ba a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

“Wannan ba zaɓe ba ne kuma duk mun san haka, a fili ta ke cewa an tafka maguɗi kuma hakan ba abin yarda ba ne.

“Hakan ba zai yiwu ba, su waye ke aika sakon taya murna ga zaɓabɓen shugaban ƙasa? Har yanzu ba mu gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ba.”

Adebanjo ya bayyana cewa ba jam’iyyarsa ta siyasa ce kaɗai ta yi Allah-wadai da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba, har ma da masu sa-ido na cikin gida da na waje da suka shaida yadda zaɓen ya gudana da ma ɗaukacin jam’iyyun adawa ba su ji daɗin yadda zaɓen ya gudana ba.

Ya kuma yi nuni da cewa maguɗin zaɓe na iya jefa ƙasar cikin rikici kamar yadda wani tsohon shugaban ƙasar ya yi kira da a soke zaɓen.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here