Hukumar sa Ido Kan Tallace-Tallace a Afirka ta Kudu ta Haramta Sanya Hoton Mata a Tallan Barasa
Hukumar da ke sa ido kan tallace- tallace a Afirka ta Kudu ta haramta tallan wata giya mai hoton mata tana mai cewa hakan bai dace ba kuma yana jawo dabi’ar fyade.
Read Also:
Hukumar ta ce irin yadda ake tallan ana nuna mace ta bude baki da shan giya ya saba wa dokokinta.
Kamfanin da ke samar da giyar a kasar ne ya sanya hoton wata mata ta bude baki tana kwankwadar giya a jikin wata mota.
Hukumar ta ce ba wai shan giyar ta hana ba, a’a yadda ake amfani da hotunan mata ne bai dace ba.
Ta ce dole a rinka mutunta mata, irin wadannan tallace- tallacen bai kamata ana sa mata ba.