Afrika: Kadan daga Cikin Kabilu Masu Al’adu na Ban Mamaki
Nahiyar Afrika tana da kabilu masu tarin yawa kuma da al’adu masu bada mamaki.
Wasu daga cikin al’adun sun samu asali ne tun kafin zuwan wayewar yankunan.
Al’adun sun hada da sharo, hawan kaho, satar matar aure, tsarkake mamaci da sauransu.
Afrika tana cike da al’adu masu tarin bada mamaki amma kuma wasu daga ciki duniya bata san da su ba.
Wasu daga cikin al’adun nahiyar masu bada mamaki sun matukar dadewa domin sun zo tun kafin wayewa. Ga wasu daga cikin ala’adun da kuma kabilun da ke yinsu.
1. Satar matar aure – Nijar
Akwai wata kabila mai suna Wodaabe da ke kasar Nijar a yammacin Afrika. An san su da satar matan junansu. A auren farko na ‘yan kabilar, ana auren zumunci ne kuma iyaye ke shirya shi tun yara suna kakana.
Amma kuma, a shagalin Gerewol na kowacce shekara, mazan kan saka kayan al’ada tare da kwalliya inda suke rawar burgewa domin satar matan wasu.
2. Tofar da yawu a matsayin gaisuwa – Kabilar Maasai
Ana samun kabilar Maasai a kasashen Kenya da Tanzani. Suna tofar wa da juna yawu a matsayin hanyar gaisuwa.
Read Also:
Baya da haka, idan aka haifa jinjiri, dole ne babban magidanci ya tofa masa yawu. A yadda suka yadda, hakan zai kare dan daga miyagun aljanu.
3. Tsarkake mamaci – Malawi
Yankin Chewa yana dauke da ‘yan kabilar Bantu da ake samu a Malawi. A yayin bikin mutuwa, al’ada ce ta dole a wanke gawar.
Daga nan sai a dauketa a kaita wani wuri mai tsarki inda ake tsaga makogwaronta sannan a zuba ruwa a wanke. Ruwan ake amfani da shi wurin dora sanwa.
4. Hawan kaho a Ethiopia
A kasar Ethiopia, samari kan yi wasu gwaje-gwaje domin tabbatar da mazantakarsu. yaro ya kan cire kaya yayi tsirara inda zai kwasa da gudu ya haye kahon namijin sanuwa.
Ana kiran wannan lamarin da Hamar.
5. Gwajin yuwuwar haihuwa a Uganda
Kabilar Banyankole karamar kabila ce a Uganda. Nauyin aure ya kan rataya a kan ‘yar uwar mahaifiyar amaryar.
A yayin da za a yi aure, kanwar mahaifiyar amarya za ta sadu da ango sannan kuma ta tabbatar da budurcin amaryar.
6. Shadi ko Sharo a kabilar Fulani
An san kabilar Fulani da shadi ko sharo kafin aure. A nan, angon zai sha duka daga wani babba a yankin domin samun mata da kuma mutunci.
Idan angon ya kasa jurewa, sai a fasa auren kwata-kwata.
7. Jan lebe – Ethiopia da Sudan
Kabilar Surma da ake samu a yankin kudancin Sudan da Kudu maso yamma na Ethiopia sun saba wannan dabi’ar.
Mata masu karancin shekaru suna tala lebensu ta yadda duk shekara zai kara girma.