Shugaba Buhari Ya Bada Sunan Farouk Ahmed a Matsayin Shugaban NPRA

 

A watan Satumban nan ne shugaban Najeriya ya nada sabon shugaban NPRA.

Bayan makonni biyu rak sai aka ji an canza Sarki Auwalu da Farouk Ahmed.

Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisa wasika, yana so a tantance Ahmed.

Abuja – Premium Times tace shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Farouk Ahmed a matsayin shugaban sabuwar hukumar man fetur na kasa NPRA.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Alhaji Farouk Ahmed zai canji Sarki Auwalu wanda kafin yanzu aka bada sunansa a matsayin sabon shugaban NPRA.

A ranar 16 ga watan Satumba, 2021, aka tura wa majalisa sunan Sarki Auwalu, ana neman a tantance shi a kujerar NPRA, da rabon dai ba zai rike mukamin ba.

Bayan ‘yan kwanaki sai fadar shugaban kasa ta bada sunan wani dabam, ya maye gurbin Auwalu.

Meyasa Buhari ya canza Sarki Auwalu?

Ba tare da yin wani bayani a wasikar ba, shugaba Muhammadu Buhari ya bada sanarwar nada Farouk Ahmed. A yanzu ana jiran majalisar dattawa ta tantance shi.

A sabuwar wasikar, shugaban kasar ya bayyana wa Sanatoci cewa ya canza wanda ya ba kujerar ne kamar yadda sashe na 34(3) na dokar mai ta PIA 2021 ta tanada.

A shekarar banan nan ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan dokar mai ta PIA da aka dade ana jira.

Jaridar tace na-kusa da masu rike da madafan iko suna kokarin ganin mutanensu sun samu mukamai masu tsoka a hukumomi da ma’aikatan fetur na tarayya.

Ganin yadda ake da kyakkyawar alaka tsakanin mai girma shuaban kasa da majalisar tarayya, ana sa rai ba da dade wa ba Sanatoci za su tantance nadin Ahmed.

Da zarar ‘yan majalisa sun tantance shugaban hukumar ta NPRA, zai shiga ofis. Jaridar PM News tace an karanto wasikar shugaban kasar a majalisa a ranar Talata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here