Karatun Bogi: Ma’aikatan Jinya ‘Yan Najeriya na Fuskantar Tuhuma  a Amurka

 

Hukumar kula da ayyukan ma’aikatan jinya ta Texas da ke Amurka ta fitar da jerin sunayen mutum 75 da ake gudanar da bincike a kan su saboda gabatar da shaidar karatu ta bogi – 43 daga cikinsu ƴan Najeriya ne.

A cewar bayanin da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet kan binciken da ake gudanarwa, mutanen da suka samu shaidar kammala karatun na bogi sun yi amfani da shi wajen samun aikin jinya.

Bayan kammala jarabawar, mutanen sun samu lasisin yin aikin jinya a jihohi da dama.

Hukumar ta ce ta shigar da ƙara kan ma’aikatan jinyar saboda takardun bogin.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta bayyana cewa hukumar kula da lafiya ta Amurka da sauran hukumomin tabbatar da tsaro sun ɗauki matakin kama mutanen da suke sayar da shaidar digirin aikin jinya na bogi.

Hukumar ta ce tana aiki tuƙuru da hukumomin da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike tare da warware matsalar nan kusa har da neman a ƙwace lasisin da suka samu ta haramtacciyar hanya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here