Tsawaita Shekarun Ritaya: Ma’aikatan Faransa Sun Shiga Yajin Aiki
Ma’aikata a Faransa sun soma wani yajin aiki a karo na biyu a fadin kasar kan shirin Shugaba Emmanuel Macron na mayar da shekarun da ma’aikatan kasar za su yi ritaya zuwa shekara 64 daga shekara 62.
Read Also:
Kungiyoyin kwadago takwas ne suka tsunduma cikin yajin aikin, matakin da ya haifar da matsaloli ga dalibai masu son zuwa makaranta da bangaren sufuri da kuma na matatun mai na kasar.
Fiye da mutum miliyan daya ne ya fito a ranar farko ta wannan yajin aikin a farkon wannan watan. Rabin malaman makarantar firamaren Faransa na cikin masu yajin aikin.
Gwamnatin Mista Macron ta dage kan shirinta na kaddamar da sauye-sauye kan dokar biyan fansho na kasar duk da cewa ra’ayin al’ummar kasar da aka dauka na cewa ba su goyi bayan matakin gwamnatin ba