Bayan Kashe Shi: Ma’aikatan Gidan Gona Sun Jefa Gawar Ubangidansu a Cikin Rijiya

 

Wasu ma’aikatan gidan gona da ke yankin Kuje na babban birnin tarayya sun kashe ubangidansu.

Ma’aikatan da ke aiki karkashin matashin mai suna Aliyu Takuma sun kashe shi sannan suka jefa gawarsa a cikin rijiya da ke kusa da gonarsa.

Hakazalika, makasan nashi sun kuma sace wasu daga cikin dabbobin mamacin da suka hada da tumakai da shanaye 40

Abuja- Rundunar yan sanda a Abuja sun bayyana yadda ma’aikata da ke aiki karkashin wani manomi mai suna Hussaini Aliyu Takuma suka kashe shi sannan suka jefar da gawarsa cikin wata rijiya da ke kallon gonarsa.

Lamarin ya afku ne a garin Jeida da ke yankin Kuje na babban birnin tarayya Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.

An tattaro cewa manomin ya bata daga gonarsa tun a ranar 2 ga watan Yuni, amma bayan an gudanar da bincike da kyau, sai aka gano cewa an kashe shi ne sannan aka jefa gawarsa a rijiya.

Sahara Reporters ta rahoto cewa hedkwatar yan sandan Kuje a ranar Asabar, ta ciro gawar Hussaini daga rijiyar, inda aka dauke shi zuwa babban asibitin gwamnati na Kuje domin bincike.

Da take tabbatar da lamarin, mataimakiyar kakakin yan sandan babban birnin tarayya, Oduniyi Omotayo, ya bayyana cewa yan sandan yankin Kabusa da ke Abuja sun kama makasan yayin da suke hanyarsu ta zuwa Kano da dabbobin da suka sace mallakin marigayin.

Omotayo ta kuma bayyana cewa ana kan gudnar da bincike kan lamarin kuma za a sanar da jama’a sakamakon binciken a kan lokaci.

Ta ce:

“Dan uwan marigayin ne ya kai rahoton lamarin hedkwatar yan sanda ta Kuje a ranar 4 ga watan Yunin 2022, cewa dan uwansa ya bar gida a ranar 2 ga watan Yuni, 2022, zuwa gonarsa amma bai dawo ba.

“Yan sanda sun shiga aiki, inda suka shiga bincike kan lamarin, an kama mutum biyu da suke aiki a gonar marigayin a yankin Kabusa yayin da suke hanyarsu ta zuwa Kano da dabbobin da suka sata mallakin marigayi ubangidan nasu.”

Kakakin yan sandar ta kara da cewar bayanan da suka samu daga wadanda suka kashe mutumin ya kai ga gano gawar Takuma a cikin rijiyar.

Majiyoyi sun bayyana cewa kimanin tumakai 40 da akuyoyi shida ma’aikatan gonar suka sace bayan sun kashe ubangidan nasu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here