Ma’aikatan Gwamnati Sun Shiga Yajin Aiki a Zimbabwe
Ma’aikatan gwamnati a Zimbabwe sun fara yajin aikin gargadi na kwana biyu domin neman karin albashi.
Ma’aikatan dai na bukatar gwamnatin kasar ta rika biyansu albashi da dalar Amurka, a maimakokn kudin kasar wanda darajarsa ke ci gaba da faduwa.
Read Also:
A wannan watan ne dai gwamnatin kasar ta ninka musu albashi, to amma kunkiyoyin kwadogon kasar sun ce hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kashi 190 cikin dari ya shafe karin albashin da aka yi musu.
Kungiyoyin kwadagon sun shaida wa BBC cewa makarantu da asibitocin da ma’aikatun gwamnati za su kasance a rufe.
A kasar Zimbabwe matsakaicin ma’aikaci na samun albashin dala 200 a wata.
To amma darajar kudin kasar ya fadi da kashi 50 cikin 100 tun watan Janairu.