Ina Aiki ne Don Cigaban Kasa – Bukola Saraki
Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce lokacin ya na kan kujerarsa, yana daukar matakai ne don cigaban kasa.
A cewarsa, har kin tabbatar da wasu mutane suka yi a kan kujerunsu saboda ba su tabbatar da nagartarsu ba, kuma sun yi hakan ne don cigaba.
A cewarsa, su na gayyatar shugabannin tsaro da sifeta janar don su tattauna da su don tabbatar da tsaron Najeriya ba don kansu ba.
Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce lokacin yana kujerarsa, bai tabbatar da wasu daga cikin wadanda Shugaba Buhari ya nada ba, saboda bai amince da nagartarsu ba.
Read Also:
Saraki ya fadi hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake mayar da martani ga Momodu, mawallafin mujallar Ovation, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Momodu ya bayyana tsohon gwamnan Kwara a matsayin shugaban da yafi ko wanne shugaba kaifin tunani a Najeriya.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce lokacin yana shugabancin majalisar dattawa, su na daukar mataki ne saboda gaba daya kasa ba wai don farin cikinsu ba.
“Kamar yadda nake yawan fadi lokacin ina tare da shugaban kasa, muna daukar matakai ne saboda cigaban kasa, ba wai don son zuciyoyinmu ba.
“Bamu tabbatar da wasu a kan kujerunsu ba, saboda tsantsaininmu. Lokacin da muka gayyaci shugabannin tsaro da sifeta janar na ‘yan sanda, mun yi hakan ne don samar da mafita ga matsalolin rashin tsaro a lokacin, ba wai don kanmu ba,” yace.