Ba ka da Aiki Sai na Tambayar Abinci ba Tare da Fita Aiki ko Kawo Gudunmawar Komai ba – Mata ga Mijinta

 

Wata mata ta ja hankali sosai a TikTok bayan ta gabatarwa mijinta da kwano babu abinci a ciki a wani bidiyo da ya yadu.

Ta dangwaran masa da rufaffen kwanon a kan teburin gabansa sannan ta bukaci da ya fita ya nemi aiki, tana mai cewa bai san komai ba sai ci.

Masu amfani da TikTok da dama sun sanya baki cikin lamarin yayin da suka bayyana ra’ayoyinsu.

Masu amfani da TikTok sun yi martani ga wani bidiyo na wata mata da ta gabatarwa mijinta kwano wayam babu abinci a ciki.

A cikin bidiyon, mutumin ya zauna yana jiran a kawo masa abincinsa, kawai sai gashi an dangwaran masa da kwano babu komai.

A cewar matar, mutumin bai da wani aiki sai na tambayar abinci ba tare da fita aiki ko kawo gudunmawar komai ba.

Ta bukaci mutumin da ya je ya nemi aiki don ya fara kawo nasa gudunmawar. Mutumin ya kadu da abun da matar tasa tayi.

Jama’a sun yi martani Koda dai bidiyon ya yi kama da zolaya, mijin ya ci fuska kuma hakan ya janyo martani.

Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

@user6042534519611 ya ce:

“Kara yaji dan Allah.”

@tracyannandem ta yi martani:

“Malami ki ba mutumin cokali mai yatsu kuma ina nikakken timatir da yaji.”

rose_pro6 ta ce:

“Kwarai kwarai idan namiji baya aiki baya cin abinci.”

@Candy ta yi martani:

“Bani da matsala da miji mara aiki ina dai da matsala da mijin da ke jin dadin rashin aikin.”

@Vera Tull ta ce: “Yayi maki kyau yarinya, yana da waya amma bai da aikin yi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here