Kotu ta Hana Magoya Bayan Peter Obi Haduwa a Kofar Lekki Toll Gate

 

An yi karar Peter Obi da magoya bayansa kan shirin gudanar da zanga-zangar #Obidatti23 Forward Ever a Legas.

Lauyan da ya kai kara zuwa kotu ya roki Alkali ya hana ‘Yan Obidients haduwa a kofar Lekki, kuma kotu ta yarda.

Kotu ba ta amincewa magoya bayan Obi su taru a kofar ba, sai dai su wuce zuwa wasu wuraren domin tattakinsu.

Lagos – Babban kotun tarayya da ke zama a garin Legas, ta yanke hukunci a karar da aka kai magoya bayan Peter Obi wadanda aka fi sani da Obidients.

‘Yan Obidients sun bukaci suyi tattaki domin nuna goyon bayansu ga Peter Obi/Datti Baba-Ahmed. This Day tace Alkali ya raba wannan gardama a yau.

Alkali mai shari’a Daniel Osiagor ya saurari karar, kuma ya halattawa magoya bayan ‘dan takarar shugaban kasar na LP yin tattaki kamar yadda suke so.

Amma Alkalin yace masu shirin wannan tattaki na #Obidatti23 Forward Ever a ranar 1 ga watan Oktoba, ba su da hurumin da za su taru a kofar Lekki.

Ba za a dankare a kofar Lekki ba

A hukuncin da kotu ta zartar, masu wannan tattaki na musamman za su iya bi ta wannan kofa da ke garin Legas, amma ba za su taru a wurin ba.

Osiagor ya bada dama ayi amfani da shahararriyar kofar ta Lekki a matsayin hanyar da za a wuce yayin tattakin #Obidatti23 domin a isa gadar Falomo.

Har ila yau, The Nation ta rahoto Alkalin yana bada umarni ga Shugaban ‘yan sanda na kasa da kwamishinan ‘yan sanda na Legas su sa ido a ranar.

Hukuncin da aka zartar a ranar Laraba yana nufin ba za a kyale mutane su taru a kofar Lekki toll gate ba, amma za a iya binta zuwa wasu wuraren.

A karshen zaman da aka yi, kotu ta daga kara sai zuwa ranar 4 ga watan Nuwamban 2022.

A wannan kofar da ke Lekki ne mutane suka shirya zanga-zangar #EndSARS a 2020. An zargi sojoji da buda wuta, amma ba a iya tabbatar da zargin ba.

Lauyoyi suna kara kan #OBIDATTI23

Kwanakin baya an ji labarin yadda wasu mutane suka dauki hayar Lauya a kotu da nufin a dakatar da tattakin ‘#ObiDatti23 Forward Ever’ da za ayi.

Mabiya Peter Obi sun niyyar yin gangami domin nuna goyon bayansu ga ‘dan takaran LP. Sai dai ana gudun hakan ya zama barazana ga tsaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here