Alakar da ke Tsakanina da Tauraron Kwallon Kafa, Ahmed Musa – Ali Nuhu
Ali Nuhu ya bayyana cewa Allah ne ya hada jininsu da tauraron kwallon kafa Ahmed Musa har suke abota.
Jarumin na Kannywood ya yi watsi da hasashen mutane na cewa yana bin tauraron kwallon ne don ya fi sa abun hannu harma wasu suka ce ubangidansa ne.
Ali ya ce babu ruwan abota da girma ko wani abu kawai idan har mutum yana da tunani da hankali za a iya abota da shi.
Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood, ya bayyana gaskiyar alakar da ke tsakaninsa da tauraron kwallon kafa, Ahmed Musa.
Mun fara magana da Ahmed Musa ta soshiyal midiya ne, Ali Nuhu
A wata hira da jaruma Hadiza Aliyu Gabon ta yi da shi a shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’, ta tambayi Ali kan yadda aka yi suka fara alaka da Ahmed Musa sai ya ce mata:
“Ahmed Musa wani mutum ne wanda zan ce mun hada halaka ta Jos da shi da yake asalinsa daga Jos yake kuma ni na yi karatu a Jos. Don haka da muka shigo bangaren nishadantarwar nan, koda dai na girme shi a shekaru kuma ni na fara harkar nishadantarwa da wuri kafin ya shigo.
“Ana nan ana nan a soshiyal midiya muka fara magana da shi, muka zo muka hadu na kai mashi ziyara, ya kai mun ziyara a haka ne amincinmu ya fara da shi.”
Read Also:
Ahmed Musa ba Ubangida na bane, abota ce tsakaninmu, Ali Nuhu
Kan tambaya da tayi cewa wasu na tunanin shi yaron Musa ne saboda ya fi shi shi samu a matsayinsa na tauraron kwallon kafa, Ali ya ce kawai dai Allah ya hada jininsu ne Sannan ya musanta cewar shi yaronsa ne domin a cewarsa shima gwani ne a fanninsa na fim kuma yana da kamfani nasa na kansa don haka babu yadda za a ce shi yaron wani ne da ke wani bangare daban ba na fim ba.
Ali ya ce:
“Gaskiya jin wannan abun zai bani dariya, akalla zan kai kimanin wajen shekara ashirin da wani abu a wannan harkar na masana’antar fim, toh mutumin da ya yi shekara kusan ashirin yana a masana’antar fim kuma a fannin sana’arsa da aka san shi yana sharafi, yana da kamfani yana da mutane karkashinsa da sauransu, ina jin ba za ka kalle shi ka ce mashi yaron wani bane.
“Eh zai iya zama yana da ubangida a cikin masana’antarsa da yake ciki, da yake a nan ya fara amma ko kuma ka je wani fage ka ce yana da ubangida a wannan wajen ina jin zai yi wahala.
“Abu na biyu kuma, ra’ayi na abota abu ne wanda ba shekaru ake dubawa ba idan yau ka samu mutum wanda ka girme shi ko ya girme ka amma kuma kowa yana da tunani da nazarin da za a iya kallon juna a dunga tattaunawa, a fahimci juna a kan rayuwa sannan kuma wasu abubuwa da suka shafi ci gaba na rayuwa har za a iya tattauna su idan ta kama ma har kasuwanci ayi da wasunsu ai ina ganin abota ta kullu.”