2020: Al’amura 5 da Suka Cakude a Siyasar Najeriya
Daga massasarar tattalin arziki zuwa rashin tsaro da ya laƙume rayuwa zuwa siyasa inda kowanne ke burin ganin shi ya kai labari.
A ɓangaren siyasa, mun zaƙulo abubuwan da suka faru kuma suka shiga tarihin siyasar Najeriya, kamar yadda Vanguard ta rawaito
1. Sauke Oshiomhole daga shugabancin APC da rikicinsa da Obaseki
Duk da cewa rigimar shugabancin jam’iyyar APC da Oshiomhole ke yi, ya faro tun Disamba 2019 inda wasu shugabannin jam’iyyar a matakin mazaɓu suka sanar da dakatar da shi, tsohon shugaban ya cigaba jagorancin jam’iyyar har 4 ga watan Maris lokacin da babbar kotun Abuja ta tabbatar da dakatarwar.
A 25 ga Yuni ne kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya ruguje shugabancin tsagin Oshiomhole. Rugujewar da ta baiwa Gov. Mai Mala shugabancin riƙo jam’iyyar.
Ana ganin Gwamnan Edo, Mr Godwin Obaseki ne kanwa uwar gamin dakatar da Oshiomhole. Da rikici ya ƙi karewa, Obaseki ya bar jam’iyyar ya karbi tikiti a PDP don tsayawa takarar gwamna.
Ana zaben Gwamna a Edon kallon zakaran gwaji kan zaɓe mai zuwa na 2023, ana ganin kamar zaɓe ne tsakanin masoya da masu adawa da Tinubu.
2. Sake naɗa shugaban hukumar zabe
Read Also:
An sake naɗa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban Hukumar zaben ran 27, 2020. Tun 1999 babu wani shugaban hukumar da aka sake mayar da shi muƙamin shugabancin wannan hukumar.
Wannan naɗi ya fuskanci martani mai zafi daga yan Najeriya da wasu yan siyasa.
3. Sauya Shekar Gwamna Dave Umahi
Lokacin da gwamnan jihar Ebonyi ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC cikin watan Nuwamba 17, ya zama batun tattaunawa a ko’ina da ma kafafen sada zumunta.
Ana ganin canza shekar tashi, bata rasa nasaba da yana yunkurin neman kujerar shugabancin ƙasar ne. 4. Rikicin Bala Muhammad da Yakubu Dogara.
2020 shekara ce da gwamnan jihar Bauchi ya samu sabani da babban amininsa, Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai.
Rikicin ya tilastawa Dogara barin jam’iyyar PDP ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
Cikin shekarar ne dai aka kama Obadiah Mailafiya, mai ritaya, tsohon ɗan takarar shugabancin kasar, lamarin da wasu ke masa kallon saboda addinin sa ne.
5. Sanata Abbo ya koma APC
Matashin sanata, Ishaku Abbo, wanda aka zaba a karkashin tutar inuwar Jam’iyyar PDP ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC tare da bayyana cewa ya bar PDP ne saboda jam’iyyar ta mutu.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan kasafin kudin sabuwar shekarar 2021.