Algeriya na Shirin Sasanta ECOWAS da Sojojin Nijar
Babban jami’in diflomasiyyar Aljeriya ya fara wata ziyarar aiki zuwa kasashen yammacin Afirka ranar Laraba a wani yunkuri na neman mafita bayan juyin mulkin da aka yi a makwabciyarta Nijar
Aljeriya ba ta goyon bayan duk wani matakin soji a Nijra.
Shugaban ƙasar Abdelmadjid Tebboune ya buƙaci ministan harkokin wajen ƙasar Ahmed Attaf ya je Najeriya da Benin da Ghana domin tattaunawa da mahukuntan ƙasashen, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta wallafa a shafinta na X.
Read Also:
Ecowas ta ce watakila za ta yi amfani da karfin soji wajen mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda sojojin ƙasar ke tsare da shi tun ranar 26 ga watan Yuli.
Aljeriya mai iyaka da Nijar ta ce yin amfani da karfin sojoji ba zai magance matsalar ba, inda shugaba Tebboune ya ce hakan zai cutar da Aljeriya kai tsaye.
Shugaban ƙasar ya yi imanin cewa Aljeriya ce ta farko da lamarin juyin mulkin Nijar din ya shafa.
A ranar Talata ƙungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Nijar har sai an sake samun gwamnatin farar hula.
Aljeriya ce kasa mafi girma a Afirka kuma tana kan iyaka da Libya da Mali, dukkansu suna fuskantar rikici tsawon shekaru.