Sarkin Musulmai, Sa’ad Abubakar ya Sanar da Ranar Alhamis 13 ga Watan Mayu 2021 a Matsayin Ranar Sallah
Sanarwar kwamitin ganin wata a Najeriya ta bayyana cewa, ba a alamar watan Shawwal ba.
An sanar cewa, gobe za a tashi da azumi na 30 domin cike watan Ramadanan bana da zai kai kwanaki 30.
Daga sanarwar, a fahimci cewa, Alhamis, 13 ga watan Mayu za ta kasance ranar karamar sallah.
Read Also:
Kwamitin Sarkin Musulmi kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun sanar da cewa ba su samu labarin ganin watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadana.
Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.
Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.
Sanar da Legit.ng Hausa ta gano a shafin kwamitin na Tuwita ya karanta: “Babu alamar ganin watan Shawwal a Najeriya yau Talata 11 ga Mayu, gobe Laraba 12 ga Mayu shi ne 30 ga Ramadan. Nan gaba kadan za a fitar da wata sanarwa a hukumance daga majalisar.