Alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta Daukar wa Tubabbun Mambobin Boko Haram

Gwamnatin tarayya ta ɗauki alkawarin inganta rayuwar tubabbbun mambobin Boko Haram su tsaya da kafafunsu.

Farfesa Yemi Osinajo ya ce gwamnati ta shirya samar wa tubabbun hanyoyin kudin shiga na halak da wurin zama.

Gwamna Zulum ya yi kira ga gwamnati ta taimaka musu wajen kammala maida yan gudun hijira gidajen su.

Borno – Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tabbatarwa tubabbun mambobin Boko Haram cewa gwamnatin tarayya zata taimaka musu.

Daily Trust ta rahoto cewa Osinbajo ya alkwarta wa tubabbun yan ta’addan cewa gwamnatin zata sama musu hanyoyin kuɗin shiga na halak domin su fara sabuwar rayuwa.

Yan ta’addan da suka miƙa wuya sun yi wa Osinbajo kyakkyawar tarba yayin da yakai musu ziyara a sansanin mahajjata dake Maiduguri ranar Alhamis.

Mataimakin shugaban ƙasan ya kai ziyarar aiki jihar Borno ne domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Zulum ta kammala.

Osinbajo ya ce:

“Ni ne shugaban kwamitin da gwamnati ta kafa, kuma mai girma gwamnan Borno, Babagana Zulum, shi ne mataimakin shugaba.”

“Zamu yi aiki tare da ku, gwamnatin jiha, da hukumomin bada tallafi domin samar muku da abubuwan rayuwa, ba kuɗin shiga kaɗai ba, har da wurin da zaku zauna da iyalanku, ku cigaba da harkokin kasuwanci.”

“Amma wajibi sai kun yi aiki da hakuri. Allah ya muku albarka, kuma ina muku fata nagari. Zamu yi iya bakin kokarin mu wajen kula da ku da izinin Allah.”

Muna bukatar taimakon FG – Zulum

Gwamna Zulum ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka wa gwamnatinsa a kokarin da take na maida yan gudun hijira gidajen su.

Ya kuma jaddada bukatar kulawa da tubabbun yan Boko Haram yadda ya kamata cikin kula da tsanaki, ya ce:

“Idan muka iya canza mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya, to nan gaba kaɗan ayyukan ta’addanci za su zama tarihi.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here