Kawo Karshen Rikicin Boko Haram: Manjo Hamaza Al-Mustapha ya Shawarci Shugaban Hafsan Sojoji

 

Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) ya shawarci shugaban hafsan sojoji kan yadda zai yaki Boko Haram.

Al-Mustapha ya bayyana bukatar a yaki Boko Haram cikin gaggawa don samun zaman lafiya a fadin Najeriya.

Ya bayyana haka ne a yau Lahadi, makwanni kadan bayan nada sabon shugaban na hafsan sojoji.

Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya shawarci Manjo Janar Faruk Yahaya, sabon shugaban hafsan soja (COAS) da ya kawo karshen rikicin Boko Haram a cikin mafi kankanin lokaci.

Al-Mustapha, wanda tsohon babban jami’in tsaro ne ga marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Lahadi, jaridar Today ta ruwaito.

Ya ce dole ne sabon hafsan sojojin ya tabbatar da hanzari wajen kawo karshen tayar da kayar baya wanda ya haifar da mummunar asara ta rayuka da dukiyoyi a sassan kasar.

“Jinkirta yaki da Boko Haram zai zama babbar illa ga Najeriya. Hanzarta murkushesu shine mafi kyau.

“Hanzari yana da matukar mahimmanci, saboda bawai muna yaki ne da aka saba ba, ana bukatar hanzari saboda ya kamata Najeriya ta farfado daga wannan yanayin cikin sauri kamar yadda ya kamata.

“Na san wannan abu ne mai yiyuwa saboda na yi wasu aikace-aikacen gida,” in ji Al-Mustapha yayin da yake taya Janar Faruk murna tare da yi masa addu’ar fatan alheri.

Al Mustapha ya kuma shawarci sabon hafsan sojojin da ya yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da nasara a yakin.

“Shawarata ita ce kada sojoji su kasance su kadai domin ba lamari ne na soja shi kadai ba. “Boko Haram ta shafe sama da shekaru 20 a iya sani na, wato tun daga daukar cikinta har zuwa girmanta.

“Idan kana son shawo kan tayar da kayar baya, duk wani bayanin ayyukansu ya kamata ya kasance a tafin hannunka, a lokacin ne za ka iya cewa ina kan makuran halin da ake ciki.

“Dole ne ka samo hanyoyinsu na samun kayan aiki, tallafi da lantarki da kuma karfinsu, abinda suke yi a kullum da kuma yadda suke samun bayanai da sauransu,” in ji shi.

Al-Mustapha ya ce dole ne hafsan sojan ya gano hanyoyin shigo da makamai zuwa cikin Najeriya sakamakon yaduwar makamai.

Al-Mustapha ya shawarci shugaban na hafsan soji ne makwanni kadan bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin mai maye gurbin marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, BBC ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here