Kungiyar Al-Qaeda ta Kashe Mutane Fiye da 70 a Mali
Fiye da mutum 70 aka kashe sannan aka jikkata wasu 200 a wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai Bamako, babban birnin Mali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun jinkirin fito da alkaluman wadanda harin ya shafa daga hukumomin Mali, wanda suka ce ya janyo asarar rayukan ɗalibai ƴan gendermerie da dama.
Read Also:
Ƙungiyar JNIM da ke alaƙa da Al Qaeda ta ɗauki alhakin kai harin a makarantar horar da sojoji da kuma filin jirage na sojoji, inda ta ce ta kashe mutane da kuma janyo asarar dukiya.
Bamako, babban birnin Mali ya kasance wuri da ba a kai wa hare-hare, amma harin na ranar Talata ya aza ayar tambaya kan tsarin tsaron sojoji da mulki a ƙasar.
Harin ya kuma sake fito da batun da shugaban gwamnatin mulkin sojin ƙasar ya faɗa na cewa sun ci galabar masu iƙirarin jihadi.
Bayan harin na ranar Talata, hukumomin Mali sun ce an ɓullo da wani shiri da zai taimakawa ɗaliban makarantar ta gendermerie da kuma iyalan waɗanda harin ya shafa.
Ƙungiyar ECOWAS ta yi Alla-wadai da harin na masu iƙirarin jihadi, inda ta nuna damuwa kan yadda hakan zai shafi zaman lafiya da kuma tsaron ɗaukacin yankin Afrika ta yamma.