Cutar Amai da Gudawa Tayi Sanadiyyar Kashe Mutane 6 a Jahar Kano
Gwamnatin jahar Kano ta tabbatar ta ce wata bakuwar cuta da ta bulla a jahar ta yi sanadin rasuwar mutane shida.
Kwamishinan lafiya na jahar, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan a ranar 7 ga watan Mayu.
Ibrahim-Tsanyawa ya ce ma’aikatar lafiya tana bincike a kan cutar da nufin gano matsalar yayin da ake jinyar sauran wadanda suka kamu.
Gwamnatin jahar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jahar, Vangaurd ta ruwaito.
Read Also:
Kwamishinan lafiya na jahar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.
Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.
“Ana danganta bullar cutar da yin bayan gida a fili da rashin tsaftace muhalli a garuruwan. “Wadanda cutar ta kamu da su suna amai da gudawa.
“Cutar ta kashe mutane shida, an sallami 28 daga asibiti yayin da sauran 18 suna nan suna jinya a asibitin,” in ji shi.
Ibrahim-Tsanyawa ya ce ma’aikatar lafiya na jihar ta fara bincike domin gano abin da ya yi sanadin wannan cutar mai daure kai.
A yayin da ya ke jadada kokarin gwamnatin jahar wurin cigaba da wayar da kan mutane da kiyayewa, Ibrahim-Tsanyawa ya bukaci mutanen garin su rika tsaftace muhallinsu da jikinsu don takaita yaduwar cutar.