Lamari Mai Cike da Al’ajabi: Amaryar da Aka Binne a Kabari an Tono ta a Raye

 

Wata amarya da aka ambata da suna Sa’adatu Hassan ta farfado bayan an binne ta a kabari.

Lamarin mai cike da al’ajabi ya afku ne a garin Kurfi da ke jahar Katsina.

An dai tono kabarin nata ne sakamakon wata mas’ala da ta taso bayan binne ta wanda likita ne ya tabbatar da mutuwarta da farko.

Wani labari mai ban al’ajabi ya kawo yadda wata amarya da aka binne bayan likita ya tabbatar da mutuwarta ta farfado bayan an tono kabarinta sakamakon wani lamari da ya taso.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wannan lamari ya afku ne a garin Kurfi da ke jahar Katsina, ana saura sati biyu daurin auren amaryar mai suna Sa’adatu.

An tattaro cewa an tono kabarin amaryar ne sa’o’i 15 bayan likita ya tabbatar da mutuwarta inda aka kuma same ta idanu biyu da ranta. Abun ya faru ne a safiyar ranar Laraba ta wannan makon.

Mazauna yankin Layin Tantan da ke garin Kurfi da suka shaida abin da ya faru da budurwar sun yi bayanin abin da ya faru.

Abin da yayi sanadiyar mutuwarta na farko

Wani mutum mai suna Alhaji Rabi’u Aliyu Maifeshi wanda ya kasance abokin mahaifin Sa’adatu ya bayyanawa jaridar cewa:

“Da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Talatar da lamarin ya afku shi ne ta wanke kayanta ne, to a wajen shanya sai ta hado da wayar lantarki, inda a nan take rai yayi halinsa.

“Nan da nan aka garzaya da ita wani asibiti mai zaman kansa domin ceto rayuwarta.

“Lokacin da aka isa asibitin, sai likitan da aka taras bayan sun yi awon da za su yi mata, suka tabbatar da cewa ta mutu.

“A takaice bayan an dawo gida an yi mata wanka da duk abin da za a yi har an sanya ta cikin makara.

“Amma saboda dare ya yi aka ce a bari da safe an yi mata janaza —Haka kuma aka yi.”

An tattaro cewa bayan an binne ta an dawo ana zaman makoki, sai wani daga cikin mutanen da suka rufe ta ya ce shi dai har yanzu yana kokwanto cewa yarinyar ta rasu.

A cewarsa a lokacin da suke sanya ta cikin kabari ya ji cikin ta yayi kugi kuma kamar da alamu har ta yi tusa. Bayan fadin haka da yayi, sai aka samu wasu ma da suka ce sun ji wannan kugi na cikinta gami da tusar, amma cewa sun yi shiru ne don gudun faruwar matsala musamman a ce ko wani abu ne na sihiri.

Wannan ne dalilin da yasa aka yanke shawarar zuwa a tone kabarin don tabbatarwa , inda aka tarar da haka lamarin yake.

Shaidu sun bayyana cewa a lokacin da wannan labari ya shiga cikin gida, sai matan da suka kwana da ita suka ce lallai suma sun ji motsi wajen makarar amma sun zata bera ne.

An riske ta a raye

Daga nan ne aka je aka tono gawarta inda aka kuma same ta a raye, idanunta a bude, sai yanayin jikinta ya canza, duk ta galabaita.

Nan take aka wuce da ita zuwa Babbar Asibitin garin Malumfashi domin sake ceto rayuwarta a karo na biyu.

Bayan an shafe kimanin sa’a daya ana kula ita a asibtin sai Allah Ya karbi ranta.

Ita dai Sa’adatu wadda ke aji biyar a babbar makarantar sakandire, saura sati biyu a daura auranta, ance ita da kanta ta raba wa kawayenta kayan baikon da aka kawo mata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here