Ambaliyar Ruwa ta Hallaka Mutane 20,ta Lalata Gine-Gine da Gadoji a Sassan Turai

Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen za ta gana da Firaiministocin ƙasashen Poland da Austria da Slovakia da kuma Jamhuriyar Czech, domin tattauna shirin Tarayyar Turai na taimakawa ƙasashen mambobinta da suka fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da ba a taɓa gani ba cikin shekaru 20.

Aƙalla mutum 20 ne ambaliyar ta hallaka.

Van da Leyen za ta yi tattaunawar ne a birnin Poland Wroclaw, inda ake sa ran ambaliyar za ta malala cikin sa’o’i masu zuwa.

Ambaliyar ruwan ta lalata gine-gine da gadoji da manya da ƙananan hanyoyi daga Romania zuwa Austria, inda ta bar dagwalon taɓo, da janyo asarar biliyoyin daloli.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Logged in as Khadija Garba. Log out?

Please enter your comment!