Ambaliyar Ruwa ta yi Sanadiyar Kashe Mutane 341 a Chadi
Aƙalla mutum 341 ne suka mutu a faɗin ƙasar Chadi sakamakon ambaliya ruwa da ƙasar ke fama da ita tun cikin watan Yuli.
Ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ambaliyar ta shafi duka lardunan ƙasar Chadi 23, yayin da kusan mutum miliyan ɗaya da rabi suka rasa matsugunansu.
Read Also:
Ambaliyar ta haifar da mummunar ɓarna a faɗin ƙasar, inda ta lalata gidaje da asarar dukiyoyi tare da dakatar da muhimman ayyuka da yanke gadoji masu yawa, lamarin da ya sa a yanzu ba a iya zuwa wasu wuraren sai da kwale-kwale.
Mutane da dama a yanzu na zaune a makarantu da wasu gine-ginen gwamnati.
Ambaliya ta shafe dubban gonaki, yayin da ta yi awon gaba da dabbobi masu yawa.
A makon da ya gabata ɗalibai 14 tare da malaminsu ne suka mutu lokacin da ginin makarantar ya rufta musu.