Ambaliyar Ruwa: Sama da Mutane 600,000 Sun Rasa Muhallansu a Somaliya
Adadin mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a Somaliya ya ƙaru da 100,000 a cikin mako guda kacal, lamarin da ya kai adadin zuwa 687,235 in ji daraktan hukumar kula da bala’o’i ta Somalia, Mohamud Moalim Abdullahi a wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Ya ce ana sa ran ruwan sama mai karfi da ya fara a ranar Talata zai ƙara dagula al’amura a kasar.
Ambaliyar ruwan ta kuma kashe mutum 50 da kuma lalata gadoji tare da mamaye wuraren zama.
Read Also:
” A ranar Asabar, hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce adadin mutanen da aka raba da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a Somaliya “ya kusan ninki biyu a cikin mako guda”, yayin da mutane miliyan 1.7 ke fama da bala’in baki daya.
“Bugu da kari, ruwan saman ya lalata hanyoyi da gadoji da filayen saukar jiragen sama a wurare da dama, lamarin da ya shafi zirga-zirgar jama’a tare da kawo ƙarin farashin kayayyakin masarufi,” in ji OCHA.
Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta Burtaniya a ranar Alhamis ta ce sama da mutane 100 da suka hada da ƙananan yara 16 ne suka mutu yayin da wasu sama da 700,000 ambaliyar ya tilastawa barin gidajensu a kasashen Kenya da Somaliya da Habasha.