Kimanin Mutane Miliyan ɗaya Ambaliyar Ruwa ta Tagayyara a Sudan ta Kudu

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 900,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a yankuna 29 na kasar Sudan ta kudu.

Ofishin kula da bayar da agaji na majalisar yankunan da ambaliyar ta fi tagayyarawa su ne jihohin Bahr El-Ghazal ta arewa, da Warrap, da Unity da kuma Western Equatoria.

Bayanin ya ce cika da tumbatsra da rafuka ke yi a garuruwan Rubkona da Bentiu na barazanar ɓalle jingar ruwa da aka gina.

Haka nan kuma ɓallewar wata gada mai muhimmanci a jihar Yammacin Bahr El-Ghazal na kawo cikas ga aikin bayar da tallafi ga mutum 50,000 da ke yankin.

Yayin da karancin kuɗi da matsalar tsaro ke ƙara dagula lamurra.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here