Ambaliyar Ruwa ta yi Ajalin Mutane 36 a Brazil
Ambaliya da zabtarewar kasa sakamakon mamakon ruwan sama mai karfin gaske a birnin Sao Paulo na Brazil sun yi ajalin mutane 36.
Akwai kuma da dama da ake kyautata zaton sun makale a ɓaraguzan gine-gine da suka rushe a garuruwan arewacin kasar.
Jiragen sojojin Brazil na ta ɗawainiyar kai jami’an ceto da likitoci yankunan da ibtila’in ya afkawa, yayin da duka hanyoyi suka lalace.
Read Also:
A yau shugaba Lula da Silva zai ziyarci yankinan da ambaliyar ta ɗaiɗaita.
Masu aikin ceto na ci gaba da kokarin sun zakulo masu sauran numfashi da kuma bude hanyoyin da suka toshe.
Gwamnatin jihar ta ruwaito cewar akalla mutum 35 ne suka mutu a birnin Sao Sebastiao, yayin da magajin garin Ubatuba ya ce yarinya Daya ta rasu.
Daruruywan mutane ne suka rasa muhallansu.
Wani jami’in hukumar kula da fararen hula ya ce akwai yiwuwar za a samu karin mutanen da suka mutu.