Ambaliyar Ruwa ta Janyo Asarar Gidaje Sama da 200 a Jihar Benue

 

Ambaliyar ruwa ta janyo asarar gidaje sama da 200 a Makurdi babban birnin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wato SEMA, Dakta Emmanuel Shior na bayyana haka a yayin raba kayan tallafi ga wadanda lamarin ya raba da muhallansu a birnin makurdi

Mista Shior ya ce wannan shi ne bala’in ambaliya ma fi muni da jihar ta taba fuskanta

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar kan wannan hali da ta shiga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here