Ambaliyar Ruwa ta Tafi da Gidaje 200 a Jihar Kebbi
Read Also:
Hukumomi a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeirya sun ce gwamman mutane ne suka rasa matsugunansu sakamakon rushewar kusan gidaje 200, bayan wata mumunar ambaliyar ruwa da aka fuskanta a yankin karamr hukumar Arugungu.
Shugaban karamar hukumar Argungu Hon. Aliyu Sani Gulma ya shaida wa BBC cewa mamakon Ruwan sama da aka fuskanta a karshen mako ne ya haifar da ambaliyar.
Ya kuma ce ambaliyar ta shafi ƙauyuka huɗu a yanikin na karamar hukumar ta Arugungu.