Ambaliyar Ruwa: Kadoji da Dama sun Kuɓuce a China
Mahukuntan ƙasar China sun bayyana cewa, wasu kadoji sun tsere daga wani gandu da ake kiwata su a kudancin ƙasar, lokacin da guguwar Haikui ta haddasa ambaliya.
Kadoji kusan 75 ne suka kuɓuce lokacin da wani tafki mai suna Maoming a lardin Guangdong ya yi ambaliya.
Yayin da aka kame wasu, hukumomin yankin sun ce sun harbe wasu “saboda tsaro”.
Read Also:
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ba da rahoton cewa, ya zuwa yanzu an tattara dabbobin guda takwas.
An gargaɗi mazauna ƙauyen da ke kusa da lardin, su zauna a gidajensu.
Guguwar Haikui ta shafe sama da mako ɗaya tana ɓarna a kudancin Asiya, inda ta shafi China da Hong Kong da Taiwan da kuma Japan.
Mutum 7 ne suka mutu yayin da wasu uku suka ɓace bayan guguwar kuma ta haddasa zabtarewar ƙasa da ambaliya a kudancin China.