Ambaliyar Ruwa ta Kashe Mutane 10 a Jihar Adamawa

 

Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wata mummunar Ambaliya da ta tashi mutanen kauyuka da dama.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ya ce sama da mutum 2,000 lamarin ya raba da gidajen su.

Wannan na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan NiMeT ta yi gargaɗin yuwuwar samun ambaliya a wasu jihohi.

Adamawa – Gwamnatin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wata mummunar ambaliyar Ruwa da ta auku sakamakon mamakon ruwan sama.

Daily Trust ta rahoto cewa mazauna yankin sun bayyana cewa Ambaliyar ta laƙume kananan kauyuka da dama a ƙaramar hukumar Girei, inda ta yi sanadin rushewar gidaje da lalacewar gonaki.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, (ADSEMA), Dakta Sulaiman Muhammadu, ya bayyana adadin mutanen da suka rasa muhallansu da mutum 2,538.

Ya ce hukumar ba da agaji zata fara kai kayan tallafi na rage radadi zuwa yankun da lamarin ya shafa domin taimaka wa mutanen da suka rasa matsugunan su, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Dr. Muhammada ya ce har yanzun ba’a gano gawarwakin wasu mutum uku da suka nutse ba, yayin da wasu ƴan mata uku da suka jikka sanadin al’amarin, yanzu haka an sallame su daga Asibiti.

Bugu da ƙari, shugaban ADSEMA ya ce ma fi yawan mutanen da ke zaune a ƙauyen Jabi Lamba da wasu ƙauyula da ambaliyar ta mamaye sun koma rayuwa da yan uwan su a wasu garuruwan.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a makon da ya gabata, hukumar hasashen yanayi ta ƙasa NiMet, ta yi gargaɗin cewa da yuwuwar wasu jihohi su fuskanci Ambaliyar ruwa a yan kwanakin nan.

Jihohin sun haɗa da Sakkwato, Bayelsa, Bauchi da kuma Jigawa. A baya Jigawa ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 50 sakamakon Ambaliya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here