Ambaliyar Ruwa: Mutane 10,000 sun Bace a Libya
Kimanin mutum 10,000 ne ake tunanin sun bace sakamakon ambaliyar ruwa a Libya, a cewar wani jami’in kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent International (IFRC).
“Za mu iya tabbatarwa daga majiyoyin mu masu zaman kansu cewa adadin wadanda suka ɓata ya kai 10,000 kawo yanzu,” in ji Tamer Ramadan, shugaban tawagar IFRC a Libya.
Read Also:
Ambaliyar ruwan da zaftarewar kasa sakamakon mamakon ruwan sama ya lalata hanyoyi da gidaje da dama.
Wurin da abin ya fi shafa shi ne tashar jiragen ruwa ta Derna, wadda yawanci tana ƙarkashin ruwa bayan da madatsun ruwa biyu da gadoji hudu suka ruguje.
Ramadan ya ƙara da cewa, adadin waɗanda suka mutu yana da yawa kuma yana iya kaiwa dubbai.
Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba IFRC na iya ƙaddamar da neman tallafin gaggawa don taimakon waɗanda ambaliyar ruwan ya shafa.