Ambaliyar Ruwa ta Tafi da Gidaje da Dama a Jalingo

 

 

Mamakon ruwan sama ya shanye gidaje da dama a Jalingo, babban birnin jihar Taraba a safiyar ranar Litinin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Lamarin ya faru ne a lokacin da kogin Mayo Gwoi ya malalo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka ɗauki tsawon sa’o’i biyu ana tafkawa.

Gidajen da ambaliyar ta shafa suna kusa da gabar kogin.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma ambaliyar ta lalata dukiya da suka haɗa da kayan gida da kuma kayayyakin abinci na miliyoyin naira.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here