Adadin Yawan Mutanen da ke Amfani da Intanet a Jihar Kano

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta ce layukan wayar salula miliyan 222.6 ake da su a ɗaukacin Najeriya a ƙarshen shekara ta 2022.

Alƙaluma sun nuna cewa an samu ƙarin layukan wayoyin salula miliyan 27.1 a kan miliyan 195.5 da ake da su a ƙarshen 2021.

Hukumar ƙididdiga ce ta fitar da alƙaluman a cikin bayananta kan masu amfani da wayoyin tarho a cikin wani rahoto na watanni ukun ƙarshe shekara ta 2022.

Rahoton ya kuma ce jimillar masu amfani da intanet sosai ya kai miliyan 154.9 a ƙarshen 2022, idan an kwatanta da miliyan 142 da ake da su a ƙarshen 2021.

Game da ƙididdigar masu amfani da wayoyin salula a tsakanin jihohi, rahoton ya nuna cewa Lagos ce jiha mafi yawan layukan wayar salula da 26.5 a ƙarshen 2022, sai jihar Ogun da ke biye mata da miliyan 13.

Kano ce jihar da ta zo a mataki na uku da layukan wayar salula miliyan 12.4.

Rahoton ya nuna cewa jihar Bayelsa mafi ƙarancin layukan wayar salula da miliyan 1.6 sai jihar Ebonyi mai layukan waya miliyan 1.9, akwai kuma jihar Ekiti mai layuka miliyan biyu.

Haka zalika, ya nuna jihar Lagos ce mafi yawan masu amfani da intanet da miliyan 18.7 sai jihar Ogun mai miliyan 9.2 sai kuma jihar Kano mai miliyan 8.5.

Bayelsa ce jiha mafi ƙarancin masu amfani da intanet da miliyan 1.1, tana ƙasan Ebonyi mai miliyan 1.3 ga kuma Ekiti mai miliyan ɗaya da rabi.

Rahoton ya nuna cewa mafi yawan masu layukan wayar salula a Najeriya da MTN suke aiki a shekara ta 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here